Hukumar Kastam ta cafke Buhunan Shinkafa, Sukari da Tabar wiwi a jihar Sakkwato

Hukumar Kastam ta cafke Buhunan Shinkafa, Sukari da Tabar wiwi a jihar Sakkwato

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana mun samu rahoton cewa, Hukumar Kastam reshen jihar Sakkwato, ta cafke buhunan shinkafa 517, dauri 320 masu nauyin kilo guda na tabar wiwi da aka yo fasakaurin su zuwa Najeriya.

Shugaban hukumar na wannan reshe, Kwanturola Gimba Umar, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata.

Yake cewa, hukumar ta kuma samu nasarar cafke wasu buhunan Sukari 34 da kuma dauri kayan sanyawa na gwanjo a manyan hanyoyin daban-daban dake jihohin Sakkwato da Kebbi cikin makonnin biyu da suka gabata.

Umar ya ci gaba da cewa, wannan kaya na da nauyin haraji na kimanin N14.9m, inda aka cafke Motar kirar Volkswagen da ta yi jigilar su. Sai dai an yi rashin sa'a ba bu wanda ya shiga hannu sakamakon Mutanen dake cikin Motar tuni sun tsere abin su tare da barin wannan dukiya.

Hukumar Kastam ta cafke Buhunan Shinkafa, Sukari da Tabar wiwi a jihar Sakkwato

Hukumar Kastam ta cafke Buhunan Shinkafa, Sukari da Tabar wiwi a jihar Sakkwato
Source: Depositphotos

Shugaban hukumar ya yabawa jami'an tsaro na 'yan sanda dangane da rawar da suka taka wajen wannan nasara da aka samu ta cafke kayan fasakauri yayin da hukumar ke ci gaba da sadaukar da kai gami da jajircewa wajen tallafawa gwamnatin tarayya bunkasar tattalin arziki.

KARANTA KUMA:

Kazalika hukumar ta Kastam ta mika wannan kaya na tabar wiwi zuwa ga takwarar ta ta NDLEA, mai yaki da fataucin muggan kwayoyi, inda wani jami'nta, Al-Mustapha Aliyu, ya yi zargin an shigo da tabar wiwin ne daga kasar Ghana da kuma Jamhuriyar Benin.

A makon da ya gabata ne jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar Kastam ta yi wata gagarumar bajinta ta samar da kudaden shiga masu tarin yawa na kimanin N140.4bn cikin watan Agustan da ya gabata wanda ba ta taba samun makamacin haka ba a tarihin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel