Kin biyan albashin watanni 34: Kungiyoyin kwadago a jihar Osun za su shiga yajin aiki ranar litinin

Kin biyan albashin watanni 34: Kungiyoyin kwadago a jihar Osun za su shiga yajin aiki ranar litinin

- Kungiyoyin kwadago a jihar Osun sun gargadi gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, da cewar zasu shiga yajin aiki na kwanaki 7, wanda zai fara daga ranar litinin

- Cewar gwamnati ta biya bashin kaso 50 na watanni 34 ga ma'aikatan da ke a matakin aiki na 08 da sama da haka, wanda yayi dai dai da biyan albashin watanni 17

- Cewar gwamnati ta biya kudaden fansho na tsawon watanni 34 ga ma'aikatan da sukayi ritaya a jihar, kuma a biya su cikin gaggawa

A ranar juma'a, kungiyoyin kwadago a jihar Osun, sun sake baiwa gwamnan jihar Rauf Aregbesola, wa'adin kwanaki shiga yajin aiki na kwanaki 7, na kin biyan bashin albashin ma'aikata har na tsawon watanni 36, biyan kudaden fansho ga hukumar kula da fansho ta kasa (PFAs) da kuma kudaden hutun ma'aikata tun na watan 2016.

Wannan sanarwa ta biyo bayan yajin aikin gargadi da kungiyoyin suka shiga a makon da ya gabata, wanda daga baya ma'aikata suka koma bakin aikinsu. Sai dai a wannan karon, ma'aikatan zasu yajin aiki na kwanaki 7 wanda zai fara daga ranar litinin, mako mai zuwa.

A cikin wata wasikar da gamayyar kungiyoyin suka bayar a ranar Juma'a, ta fara kawo batun wata yarjejeniya mai taken "Yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Osun da kungiyoyin kwadago, a ranar Asabar, watan Disamba 2017", inda suka bukaci Aregebsola da ya mutunta wannan yarjejeniyar don kawo zaman lafiya.

Kin biyan albashin watanni 34: Kungiyoyin kwadago a jihar Osun za su shiga yajin aiki ranar litinin

Kin biyan albashin watanni 34: Kungiyoyin kwadago a jihar Osun za su shiga yajin aiki ranar litinin
Source: Facebook

Takardar wacce aka aikata kai tsaye ga gwamnan jihar, dauke da sa hannun shugaban kungiyar kwadago na jihar, Comrade Jacob Adekomi da kuma takwaransa na kungiyar TUC, Comrade Adebowale Adekola, na cewa: "Ranka ya dade, duba da irin wahalhalun da ma'aikata ke fuskanta, muna amfani da wannan sanrwa don sanar dakai shiga yajin aikinmu na kwanaki 7.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Wata kungiya a Daura ta tara N70m don yakin zaben Buhari da Masari

"Zamu fara wannan yajin aiki daga ranar litinin, 10 ga watan Satumba 2018, idan har ba'a biya mana bukatun da muka gabatar ba kafin zuwan lokacin"

A cewar wasikar, "Bayan dogon nazari da kungiyoyin kwadago suka yi dangane da rashin cika alkawarin da gwamnati tayi, duk da cewa mun shiga yajin aiki na kwanaki 3 a matsayin gargadi, da nufin tunasar da gwamnati bashin albashin da ma'aikata ke bi na watanni 34, da suka hada da fansho da gratuti, don haka ga bukatunmu kamar haka."

"Cewar gwamnati zata biya bashin kaso 50 na watanni 34 ga ma'aikatan da ke a matakin aiki na 08 da sama da haka, wanda yayi dai dai da biyan albashin watanni 17, kuma a biya su cikin gaggawa."

"Cewar gwamnati ta biya kaso 50 na hakkoki da wasu rarar kudade da ake baiwa ma'aikata na tsawon watanni 34, wanda yayi dai dai da biyan hakkokin watanni 17, kuma a biya su cikin gaggawa."

"Cewar gwamnati ta biya kudaden fansho na tsawon watanni 34 ga ma'aikatan da sukayi ritaya a jihar, kuma a biya su cikin gaggawa," da dai sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel