Bashin N117bn: Na bar Fayose da Allah, inji sabon gwamnan jihar Ekiti

Bashin N117bn: Na bar Fayose da Allah, inji sabon gwamnan jihar Ekiti

- Gwamna mai jiran gado, Kayode Fayemi ya ce ya bar Fayose da Allah game da batun bashin N117 biliyan da ya tara a jihar

- Fayemi ya ce shi yanzu abinda yasa a gaba shine yadda zai saukaka rayuwar mutanen jihar

- Fayemi ya ce bayan wannan bashin akwai basusukan da ma'aikata da 'yan fansho ke bin tsohuwar gwamnatin

Zababen gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi ya ce babu abinda zai yi sai dai ya bar gwamna mai barin gado, Ayodele Fayose da Allah game da bashin N117 biliyan da ya gada daga wajensa.

A yayin da yake jawabi yayin karbar rahoton kwamitin da aka kafa domin tabbatar da mika mulki ga sabuwar gwamnatin, Fayemi ya yi alkawarin fara aiwatar da ayyukan da zasu sauya rayuwar mutanen jiharsa idan ya fara aiki ranar 16 ga watan Oktoba.

Gwamnan ya ce Ofishin kula da basusuka DMO ta bayyana cewa bashin da ake bin jihar ya kara daga N18 biliyan a shekarar 2014 zuwa N117 a shekarar 2018 karkashin mulkin gwamna Ayodele Fayose.

Bashin biliyan N117: Na bar Fayose da Allah, inji sabon gwamnan jihar Ekiti

Bashin biliyan N117: Na bar Fayose da Allah, inji sabon gwamnan jihar Ekiti
Source: Depositphotos

Kwamitin ta ce bayan wannan bashin akwai albashi da allawus da fansho da kudaden sallama da ma'aikatan jihar ke bin gwamnatin Fayose.

DUBA WANNAN: Danwaken zagaye: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Shekarau da Ganduje

Fayemi ya kuma bayar da shawarar kafa doka ta musamman da zata fayyace ayyukan da gwamnati mai barin gado za tayi domin ganin anyi canjin gwamnatin cikin sauki, gwamnan mai jiran gado ya bayar da shawaran ne saboda irin wahalhalun da kwamitin ta fuskanta daga gwamnatin Fayose.

Ya ce kasashen nahiyar Afrika kamar Kenya, Ghana, Afirka ta Kudu da wasu kasashen da suka cigaba duk suna da irin waddanan kwamitocin.

"Mun san san cewa za'a samu basusuka daga gwamnati mai barin gado amma abinda ke gaban mu shine yadda zamu inganta rayuwar mutanenmu.

"Saboda haka, duka abinda gwamnatin baya ta aikata zamu bar su da Allah ya yi sakayya domin shine yasan yadda zaiyi dasu." inji Fayemi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel