Guguwar canja sheka: Mutane 15,000 sun fice daga APC sun koma PDP a jihar Benue

Guguwar canja sheka: Mutane 15,000 sun fice daga APC sun koma PDP a jihar Benue

- Akalla mutane 15,000 ne suka sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta APC a jihar Benue

- Da ya ke jawabi yayin sauya shekar, Farfesa Ityavyar ya ce wannan mataki na komawa PDP ya biyo bayan kudirinsa na hada karfi da Samuel Ortom, don ci gaban jihar baki daya.

- Da ya ke karbar wadanda suka sauya shekar, shugaban jam'iyyar PDP a gundumar Mbadede, Hon Zwa ya basu tabbacin yin adalci tare da mutuntasu ba tare da nuna banbanci ba

A ci gaba da kadawar guguwar canja sheka, musamman da ta mamaye jam'iyyar APC a jihar Benue, wannan karon, guguwar ta yi awon gaba da kwamishinan Ilimi, kimiya da fasaha, Farfesa Dennis Ityavyar, wanda ya fice daga jam'iyyar ta APC tare da wasu mutane 15,000 zuwa jam'iyyar PDP, a gundumar Mbadede, karamar hukumar Vandeikya.

Da ya ke jawabi yayin sauya shekar a jiya juma'a, 7 ga watan Satumba, Farfesa Ityavyar ya ce wannan mataki da ya dauka tare da wasu mambobin jam'iyyar APC na komawa PDP ya biyo bayan kudirinsa na hada karfi da karfe da gwamnan jihar, Samuel Ortom, don ci gaban jihar baki daya.

Farfesa Ityavyar ya ce: "Gwamna Ortom ya cancanci goyon bayan al'ummar Kunav, dama daukacin jama'ar Benue musamman yanzu da ta bayyana karara cewa kudirin makiyaya shine kashe mutane don mallake yankin Benue.

Guguwar canja sheka: Mutane 15,000 sun fice daga APC sun koma PDP a jihar Benue

Guguwar canja sheka: Mutane 15,000 sun fice daga APC sun koma PDP a jihar Benue
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin fushi idan ka yaudare shi - Lawal

"Ina so kowa ya sani cewa,a halin yanzu gwamnanmu na fuskantar kalubale daga bangarori da dama, saboda ya tsaya kai da fata akan al'ummar Kunav, ya ki amincewa wasu makiyaya da sunan Miyetti Allah su kwace yankinmu, don haka tabbas yana binmu bashi, dole mu saka masa da goyon bayanmu dari bisa dari," a cewar Farfesa Ityavyar.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar daga gundumar Mbadede, wadanda ake ganin jiga jigai ne a Arewa maso Gabashin Benue, kuma jigo a jam'iyyar APC, akwai Mr. Patrick Ikyor, Iorhuna Stephen, Fanem Lever, Elder Azua Nimbe, Iortimbir Avuve da kuma wasu da dama da ake kallonsu a matsayin jigogi a jam'iyyar.

Da ya ke karbar wadanda suka sauya shekar, shugaban jam'iyyar PDP a gundumar Mbadede, Hon Zwa ya basu tabbacin yin adalci tare da mutuntasu ba tare da nuna banbanci ba, don hada karfi da karfe wajen samun nasarar jam'iyyar a zaben 2019 da ke gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel