2019: Dalilin da yasa zan buga ragowar ‘yan takarar PDP da kasa – Saraki

2019: Dalilin da yasa zan buga ragowar ‘yan takarar PDP da kasa – Saraki

- Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya cika bakin cewar shine zai lashe zaben cikin gida na fitar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP

- Jam’iyyar PDP zata gudanar da zaben cikin gida na fitar da dan takara a ranar 6 ga watan Oktoba

- Saraki ya bayyana cewar yana da yakinin cinma burinsa na zama shugaban kasar Najeriya a 2019

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar yana da yakinin zai cinma burinsa na mulkar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP.

Jaridar Daily Trust ta rawaito Saraki na fadin cewar dole ‘yan Najeriya su tashi tsaye domin ganin Buhari ya bar gwamnati a 2019 saboda hakan ne kawai zai kawo hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya.

2019: Dalilin da yasa zan buga ragowar ‘yan takarar PDP da kasa – Saraki

Bukola Saraki
Source: Twitter

Saraki na wadannan kalamai ne yayin ganawa da ‘yan jam’iyyar PDP a birnin Owerri na jihar Imo, a cigaba da rangadin neman goyon bayan jama’a da yake yi.

A cewar Saraki, “da yardar Allah nine zan zama dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019 saboda nine mutumin zai hada kan ‘yan Najeriya da bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar habaka kasuwancin cikin gida.

DUBA WANNAN: Da walakin: Sojoji sun yi ram da wani dan majalisa a kan rikicin Jos

Kan ‘yan Najeriya bai taba rabuwa ba kamar wannan lokaci. Wasu ma kunya suke ji a kira su ‘yan Najeriya. An raba kan jama’a ta hanyar amfani da addini da kabilanci. An yi watsi da bawa wasu bangaren kasar nan dama,” a cewar Saraki.

Saraki ya kara da cewar kyawawan manufofin da yake dasu zasu bashi fifiko wajen lashe zaben cikin gida da jam'iyyar PDP zata yi ranar 6 ga watan Oktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel