Daya daga cikin masu son takarar shugaban kasa a PDP ya janye

Daya daga cikin masu son takarar shugaban kasa a PDP ya janye

- Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya sanar da cewa ya janye daga takarar shugabancin kasa na 2019

- Fayose ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayin da yake karbar bakuncin Sanata Kwankwaso da Kashim Tanimu a jihar Ekiti

- Fayose ya ce ya yanke shawarar janyewar ne saboda ya mayar da hankali wajen kwato hakkin mataimakinsa da APC ta tauye wa hakkinsa a zaben gwamna da akayi a jihar

Mun samu daga Daily Trust cewa gwamna mai barin gado a jihar Ekiti, Mr Ayodele Fayose, ya sanar da cewa ya janye niyyarsa na tsawa takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2019.

Gwamna Fayose yana daga cikin mutanen da suka fara bayyana sha'awarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP duk da cewa jam'iyyar ta nanata cewa zata fitar da dan takarar shugaban kasa a 2019 ne daga Arewa bisa tsarin karba-karba na jam'iyyar.

Fayose ya janye daga takarar shugabancin kasa a PDP, ya fadi dalili

Fayose ya janye daga takarar shugabancin kasa a PDP, ya fadi dalili
Source: UGC

Fayose ya sanar da janyewarsa ne yayin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon Minista, Kashim Tanimu suka ziyarci jiharsa domin neman kuri'insa da na deleget din jihar gabanin zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi

Ya ce ya janye niyyarsa na fitowa takarar zaben ne saboda ya mayar da hankali kan mataimakinsa, Farfesa Kolapo Olusola-Eleka wanda ya sha kaye a zaben gwamna da akayi a jihar a kwanakin baya.

"Na janye daga takarar shugabancin kasa ne saboda in mayar da hankali wajen gwagwarmayar kwato wa mataimakina hakkinsa da aka kwace a zaben gwamna da ta gabata.

"A matsayina na shugaba na gari, bai dace inyi watsi da mataimaki na da APC ta yiwa kwace ba domin neman wani mukamin.

"Fostoci ne suka kule a daki. Sai dai a yanzu ina son mayar da hankali ne wajen kwato hakin mu da aka kwace ne," inji Fayose.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel