A karon farko tun bayan barin mulki, Obama yayi jawabi kan zabukan dake tafe a Amurka

A karon farko tun bayan barin mulki, Obama yayi jawabi kan zabukan dake tafe a Amurka

- An kusa fara zabukan tsakiyar zamanin mulki a Amurka

- Ana kiransu Mid-Term Elections a inda ake zaben 'yan majalisu

- Obama yayi kira da a fito a kada Trump da jam'iyyarsa

A karon farko tun bayan barin mulki, Obama yayi jawabi kan zabukan dake tafe a Amurka

A karon farko tun bayan barin mulki, Obama yayi jawabi kan zabukan dake tafe a Amurka
Source: Getty Images

A watan Nuwambar nan mai zuwa za'a yi zabukan cike gurabu da dora sabbin yan majalisar wakilai da dattijai a majalisar Amurka.

Obama, tsohon shugaban Amurka, wanda ya bar mulki a watan Yanairun bara, yayi jawabi mai sosai rai kan yadda kai ya rabu a kasar a mukin shugaba Donald Trump.

Tsohon shugaban yayi kira da jama'a su fito kwansu da kwarkwatarsu su dangwala zabe domin korar jam'iyyar Republican daga iko da majalisu da take dashi shekaru hudu.

DUBA WANNAN: Adam Zango ya tuba gaban Ali Nuhu

Su dai a kasar Amurka, ko mai mulki yana wata jam'iyyar, jam'iyyar adawa na iya kwace iko da majalisa kuma baza kaji ana kira shuwagabannin su sauka ba, ko a tura musu jami'an tsaro su kwace iko da majalisar.

Shugaba Trump na uskantar suka daga 'yan santsi, inda kuma 'yan tabo na kasar, masu ra'ayin mazan jiya ke murna da zuwansa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel