Siyasar Kano ta dau zafi: APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019

Siyasar Kano ta dau zafi: APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019

- APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019

- Wannan alkawarin da daga cikin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla, wanda ya sa shekarau sauya sheka daga PDP zuwa APC a jiya

- A bangare daya kuwa, ficewar Shekarau daga PDP bai yiwa jiga jigan jam'iyyar dadi ba, musamman Bukola Saraki, wanda yayi kokarin dakatar da shi amma abu yaci tura

A jiya Juma'a, 7 ga watan Satumba, jam'iyyar APC ta yiwa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau alkawarin bashi tikitin tsayawa takarar sanatan mazabar Kano ta tsakiya, a zaben 2019 mai gabatowa.

Wannan alkawarin na daga cikin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla, wanda ya sa shekarau sauya sheka daga PDP zuwa APC a jiya.

Wannan kujera da APC ta yi alkawarin baiwa Shekarau, na a hannun Dr. Rabiu Musa kwankwaso, wanda shima ya ke fafutukar ganin ya damkata ga jam'iyyar PDP. Za'a iya cewa fitar Shekarau daga PDP a yanzu, ya baiwa Kwankwaso cikakken iko akan jam'iyyar a jihar.

A bangare daya kuwa, ficewar Shekarau daga PDP bai yiwa jiga jigan jam'iyyar dadi ba, musamman irin kokarin da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki yayi na ganin Shekarau bai bar jam'iyyar ba, amma hakan ta ci tura.

KARANTA WANNAN: Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

Siyasar Kano ta dau zafi: APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019

Siyasar Kano ta dau zafi: APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019
Source: Depositphotos

Rikicin PDP ya samo asali tun bayan da majalisar zartsawar jam'iyyar ta kasa ta rushe kwamitin zartaswa na jam'iyyar a matakin jihar Kano, duk da cewa kotu ta haramtawa majalisar yanke wannan danyen hukunci.

A bangaren Shekarau kuwa, a jiya shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya jagoranci wasu jiga jigan jam'iyyar zuwa jihar Kano don marabtar Shekarau a jam'iyyar. Rahotanni sun bayyana cewa APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso.

Haka zalika, daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa akwai sanya na hannun damar Shekarau cikin jagorancin APC a jihar, bashi tikitin kujerar sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2019, bashi kujerar kwamishinoni a gwamnatin Kano, bashi wasu kujerun majalisun tarayya dana jihar, da kuma bashi mukaman siyasa a gwamnatin tarayya, da dai sauransu.

Rahotanni sun nuna cewa, akwai yiyuwar APC ta baiwa Shekarau kujerun Ministoci idan har ta zarce a 2019. Wata majiya ta ce: "APC ta je Kano don rokon Shekarau ya shiga jam'iyyar, inda aka shawo kansa bayan kulla yarjejeniya."

Majiyar ta shaida cewa baiwa Shekarau tikitin sanatan Kano ta tsakiya, da kuma sauran mukamai da kujeru a matakin jiha da kasa, zai taimaka wajen gurguntar da kudirin Kwankwaso na tsayawa takarar shugaban kasa, a karshe zai yi asarar kujerar Sanatan kuma ya rasa ta shugaban kasar "yayi biyu babu ko daya kenan".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel