Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba cikin shekaru 20 masu zuwa - Bafarawa

Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba cikin shekaru 20 masu zuwa - Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa ko da za a bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari dama ta jagorantar kasar nan har na tsawon shekaru 20 masu zuwa ba zai iya gyara tattalin arzikin ta ba.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon gwamnan ya fedewa shugaba Buhari Biri har Wutsiya yayin ganawa da magoya bayan jam'iyyar PDP cikin Birnin Owerri na jihar Imo a wani bangare na ci gaba shawagin sa na yakin neman zabe.

A yayin jaddada cewa shugaba Buhari ba ya da wayewa ko ta sisin kobo ta fuskar siyasa, tsohon gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa shugaban kasar baya da wata cancanta da kwarewa bisa jagoranci da zai habaka tattalin arzikin kasar nan.

Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba cikin shekaru 20 masu zuwa - Bafarawa

Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba cikin shekaru 20 masu zuwa - Bafarawa
Source: Depositphotos

Yake cewa, a halin yanzu babban kalubalen dake fuskantar Najeriya bai wuci shugabanninta da ba su wata masaniya da kwarewa kan harkokin siyasa, inda ya ce "ba bu abinda Soja ya sani a faggen Dimokuradiyya".

KARANTA KUMA: Ni zan yi nasarar samun Tikitin jam'iyyar PDP na takarar Kujerar Shugaban kasa - Saraki

Da yake kira ga mambobin jam'iyyar akan su fidda dan takara mafi cancanta da zai iya lallasa shugaba Buhari a zaben 2019, ya bayyana cewa ba bu wani dan takara da zai iya wannan gagarumar bajintar face shi.

Ya kuma bayyana cewa nasarar shugaba Buhari a zaben 2015 ta faru ne kurum bisa yanayi na tsausayi, inda ya sha alwashin sauya fasalin kasa tare da garambawul muddin ya yi nasara ta lashe zaben 2019.

Ya kuma alakanta gwamnatin shugaba Buhari da zalunci, inda ta yi amfani da hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC wajen yi ma sa kazafi da zargi na aikata rashawa a wasu lokuta na baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel