Babu dokar da muka take don mun siyawa Buhari fam din takara – NCAN

Babu dokar da muka take don mun siyawa Buhari fam din takara – NCAN

- Kungiyar Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN), tace abunda tayi bai sabama kowani doka na kasar ba

- Kun giyar dai ta siyawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari fam din sake takara a zabe mai zuwa

- Ta nisanta kanta daga rade-radin cewa Gwamna Yahaya Bello ne ya bata kudin siyan fam din

- Shugaban kungiyar yace mambobinsu ne suka hada kudinsu

Kungiyar magoya bayan Shugaban kasa da ta siya ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari fam din takara wato Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN), tace abunda tayi bai sabama kowani doka na kasar ba.

Shugaban kungiyar NCAN na kasa, Barista Sanusi Musa wadda yayi jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 7 ga watan Satumba yayi watsi da rade-radin cewa kungiyar ta samu kudin ne daga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Babu dokar da muka take don mun siyawa Buhari fam din takara – NCAN

Babu dokar da muka take don mun siyawa Buhari fam din takara – NCAN
Source: UGC

Musa wadda yace kungiyar ta dauki lokacinta wajen nazarin doka, ya kara da cewa wannan doka da ake Magana akai ta ta’allaka ne ga hada kudade domin tallafawa dan takarar jam’iyya a wani zabe ba wai wani mutun da kawai zai zamo dan takara bayan kammala tantancewa ba.

KU KARANTA KUMA: Jihohi 12 zasu fuskanci ambaliyar ruwa – NEMA da NHISA sunyi gargadi

Akan zargin alakansu da Gwamna Bello, ya bayyana cewa bai taba haduwa da gwamnan jihar Kogin ba balle ace har ya karbi kudade daga hannunsa.

Musa wadda yace sun hada kudaden ne daga mambobinsu, ya nuna shirin kungiyar wajen gabatar da fam din ga Shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel