Dalilin da yasa na fice daga PDP - Tsohon Gwamna

Dalilin da yasa na fice daga PDP - Tsohon Gwamna

- Tsohon gwamnan Cross Rivers, Mr Donald Duke ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga PDP

- Donald Duke ya ce tsarin karba-karba da PDP ke amfani dashi wajen fitar da dan takarar shugabancin kasa yasa ya sauya sheka

- Mr Duke ya soki tsarin inda ya ce tsarin na tauye wa 'yan Najeriya ikon zabar dan takarar da yafi cancanta

Tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Donald Duke, ya ce ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa SDP ne domin yin takarar shugaban kasa saboda tsarin karba-karba da jam'iyyar ta PDP ta ke amfani dashi wajen fitar da 'yan takarar wanda bashi cikin dokar kasa.

A zaben shekarar 2019, jam'iyyar PDP za ta zabo dan takarar shugabancin kasar ta ne daga yankin Arewa, shi kuma Donald Duke daga yankin Kudu maso Kudu ya fito.

Dalilin da yasa na fice daga PDP - Tsohon Gwamna
Dalilin da yasa na fice daga PDP - Tsohon Gwamna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Danwaken zagaye: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Shekarau da Ganduje

Mr Duke ya yi wannan bayanin ne a wani rubutu da ya wallafa a yau Juma'a a shafinsa na Twitter. Tsohon gwamnan ya ce ya yi nazarin tsarin siyasar Najeriya kafin ya dauki matakin ficewa daga jam'iyyar PDP.

A yayin da yake sukar tsarin na karba-karba, Mr Duke ya ce tsarin yana tauye wa jama'a zaban shugaban da yafi cancanta muddin bai fito daga yankin da jam'iyyar zata fitar da dan takarar ta ba.

Kazalika, Mr Duke ya ce bai amince da masu ikirarin cewa jam'iyyar APC da PDP ne kawai zasu iya fitar da dan takarar da zai lashe zaben shugaban kasa ba. Ya ce ba dai-dai bane a ce kawai jam'iyyu biyu ne kawai zasu rika juya akalar kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel