An zargi hukumar FRSC da binne mutane da suka mutu a hadari kafin iyalinsu su iso

An zargi hukumar FRSC da binne mutane da suka mutu a hadari kafin iyalinsu su iso

- An zargi Road Safety da keta haqqin gawarwaki

- Suna binne gawarwakin wadanda hadari ya ritsa dasu

- Mutuware ya kamata a kai gawar wadanda ba'a sansu ba na lokaci

An zargi hukumar FRSC da binne mutane da suka mutu a hadari kafin iyalinsu su iso

An zargi hukumar FRSC da binne mutane da suka mutu a hadari kafin iyalinsu su iso
Source: Original

A kokarin jama'a na jan hankalin hukumomi masu kula da hadurra a tituna, wasu wadanda abin ya shafa, sun nuna rashin jin daqdinsu kan yadda ake saurin binne musu gawarwakin yan-uwansu da suka rasu a hadurra tun kafin su zo.

A rahoton da majiyar Legit.ng ta ji, an gano cewa a watan jiya, hadari da ya rutsa da motar bas wadda ta kama hanya daga Nasarawa zata ce Inugu tayi hadari a jihar Kogi, Peace Mass Transit da hukumar kare hadurra tayi gaban kanta kan lamarin.

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya zauna da kungiyar CAN

An dai binne gawarwakin ne 15 ga watan Augusta, kamar yadda wasu suka yi zargi.

Gawarwakin dai sun qone kurmus, inda wasu suka ce ba'a basu gawarwakin yan'uwansu ba.

Wani marubuci ma a shafin yanar gizo, Uncle Prank, yayi zargin ko asiri da tsafi wai ake yi da sassan yan'uwan nasu.

Hukumar Road Safety tace kamfanin da abin ya rutsa dasu su suka ce a binne gawarwakin tunda sun qone qurmus.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel