Ni zan yi nasarar samun Tikitin jam'iyyar PDP na takarar Kujerar Shugaban kasa - Saraki

Ni zan yi nasarar samun Tikitin jam'iyyar PDP na takarar Kujerar Shugaban kasa - Saraki

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya bayar da tabbacin sa gami da yakinin samun nasara ta lashe tikitin jam'iyyar PDP na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

A yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar da za a gudanar a ranar 6 ga watan Okotoba, shugaban majalisar ya bayyana cewa muradin sa na kasancewa shugaban kasar nan ya zarce duk wani fata domin kuwa tamkar ya riga da tabbata ne.

A sanadiyar haka ne yake kira gami da neman al'ummar kasar nan akan su jajirce wajen rusa duk wani shiri da tsare-tsaren shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kudirinsa na ci gaba da jagorantar kasar har bayan shekarar 2019.

Saraki ya kuma bayyana cewa tumbuke Buhari daga kujerar mulkin kasar nan ita kadai ce hanya da za ta tabbatar da hadin kai gami da tsaro a cikin ta, inda a halin yanzu lamarin kasar nan ya tabarbare sakamakon rikicin adini, kabilanci da kuma rashin adalci na gwamnatin Buhari.

Ni zan yi nasarar samun Tikitin jam'iyyar PDP na takarar Kujerar Shugaban kasa - Saraki

Ni zan yi nasarar samun Tikitin jam'iyyar PDP na takarar Kujerar Shugaban kasa - Saraki
Source: Twitter

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP yayin da ziyarci birnin Owerri na jihar Imo inda ya bayyana cewa, Najeriya ba ta taba kasancewa cikin rabuwar kai ta fuskar addini, kabilanci ko kuma siyasa ba tamkar wannan zamani na shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: 2019: Wasu Sanatoci 2 na jam'iyyar PDP sun sha alwashin fatattakar Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna

A cewar sa, Najeriya na bukatar shugaban kasa da zai tabbatar da hadin kan dukkanin al'ummar ta wuri guda wajen habakar tattalin arziki musamman ta fuskar tsame su daga kangi na talauci, rashin aikin yi da kuma wahalhalu na rayuwa wanda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza magancewa.

Shugaban majalisar ya kara da cewa, ba don kariya ta Mabuwayi da kuma tasirin talakawan kasar nan, tuni da shugaba Buhari ya tsige sa daga kujerar sa shekaru uku da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel