Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

- Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

- An kwato su ne daga hannun tsaffin ma'aikatan hukumar nan ta kidayar al'umma ta kasa

Kwamiti na musamman da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada domin kwato dukkan dukiyar al'ummar da wasu ma'aikatan gwamnati suka yi sama da fadi da su a cikin garin Abuja ya samu nasarar kwato motoci 19.

Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati

Buhari ya kwato motoci 19 daga hannun wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Yan bindiga sun harbe wani babban malami a Najeriya

Motocin dai kamar yadda muka samu, kwamitin ya kwato su ne daga hannun tsaffin ma'aikatan hukumar nan ta kidayar al'umma ta kasa watau National Population Commission (NPopC)a turance.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa su dai motocin tun farko an zargin tsaffin kwamishinonin hukumar ne da tafiya da su bayan da suka kammala wa'adin mulkin su duk da rashin kyautawar hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a farkon hawa bisa karagar mulki, shugaba Muhammadu Buhari a kokarin sa na ganin ya killace dukiyar al'umma daga barayi, ya kafa kwamitin da zai taimaka masa wajen kwato kadarorin gwamnati dake hannun wasu.

A wani labarin kuma, Masana a fannin ilimin kimiyya da fasaha sun bayyana cewa 'yar girgizar kasar da aka samu a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a yau din nan na iya kasantuwa ta dalilin fasa duwatsu barkatai da al'umma ke yi.

A don haka ne ma masanan sukayi kira ga mahukunta da su waiwayi batun su kuma yi kokarin samar da dokar da zata hana ayyukan fashe-fashen duwatsun ba bisa ka'ida ba domin kaucewa sake aukuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel