2019: Wasu Sanatoci 2 na jam'iyyar PDP sun sha alwashin fatattakar Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna

2019: Wasu Sanatoci 2 na jam'iyyar PDP sun sha alwashin fatattakar Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna

Wasu Sanatoci biyu masu ci karkashin inuwa ta jam'iyyar adawa ta PDP, sun sha alwashin fatattakar gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, daga kan kujerar sa ta gwamnatin jihar a yayin babban zabe da za a gudanar a shekarar 2019.

Sanata Suleiman Hunkuyi mai wakilcin jihar Kaduna ta Arewa da kuma Sanata Danjuma La'ah mai wakilcin jihar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, sun bayyana cewa za su hada karfi da karfi wajen ganin sun yi nasara akan gwamnan a yayin zaben.

A yayin da Sanata hukunci zai yi takarar sa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Sanata La'ah zai kuma yi amfani da mashahurancinsa a mazabarsa wajen marawa abokin aikin sa baya domin samun nasara ta fatattakar El-Rufa'i da zai yi takararsa a jam'iyyar APC.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Juma'a ta yau ne Sanata Hunkuyi ya bayyana kudirin sa na tsayawa takarar kujerar gwamnatin jihar Kaduna, a yayin wani taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar daga kananan hukumomi 11 da aka gudanar a unguwar Wakili dake karamar hukumar Zangon Kataf.

2019: Wasu Sanatoci 2 na jam'iyyar PDP sun sha alwashin ganin bayan Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna

2019: Wasu Sanatoci 2 na jam'iyyar PDP sun sha alwashin ganin bayan Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna
Source: UGC

Cikin jawaban sa ga magoya baya, Sanata Hunkuyi ya bayyana cewa muddin ya yi nasara a zaben to kuwa ya sha alwashin mayar da rawanin dukkanin Sarakunan gargajiya na jihar cikin mako guda da gwamna El-Rufa'i ya tumbuke, inda ya bayyana wannan lamari na gwamnan a matsayin wani nau'i na rashin adalci gami da zalunci.

KARANTA KUMA: An gurfanar da wani 'Dan 'Kwallo bisa laifin satar Dukiya a Coci

'Dan takarar ya kuma sha alwashin sake nazari da duba kan lamarin malamai 25, 000 na makarantun Firamare da gwamna El-Rufa'i ya sallama daga bakin aiki, inda zai kafa kwamiti da zai tantance su bisa ga cancanta.

Legit.ng ta fahimci cewa, Hunkuyi wanda a watan Yulin da ya gabata ne ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP sun shiga takun saka da gwamna El-Rufa'i da ta yi tsananin gaske cikin watan Mayu sakamakon sabanin ra'ayoyi da akida irin ta siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel