Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

- Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

- Lamarin ya auku ne a garin Awka, jihar Anambra

- Har yanzu ba a san halin da faston yake ciki ba

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa wasu 'yan bindiga dadi da ba'a san ko suwaye ba sun yi wa wata majami'a a garin Awka na jihar Anambra dirar mikiya inda kuma suka harbe faston cocin.

Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya

Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun harbe babban malamin addini a Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Buhari

Kawo zuwa hada wannan labarin dai majiyar mu ta ce ba'a gama tantance ainihin halin da faston yake ciki ba biyo bayan kai shi wani boyayyen wuri da mabiyan sa sukayi.

Legit.ng dai ta samu lamarin dai ya faru ne da marece a garin na Awka dake zaman babban birnin jihar ta Anambra kuma kusa da ofishin 'yan sanda a unguwar da lamarin ya auku.

Wasu shaidun gani da ido dai sun ce 'yan bindigar wadanda har yanzu ba a san ainihin takamaiman dalilin aikata ta'asar ta su ba sun samu faston ne a kafafuwa da harbin bindigar tasu.

A wani labarin kuma, Jami'an sojin Najeriya na rundunar Lafiya Dole dake fafatawa da 'yan ta'addan Boko Haram a yankunan jahohin Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana samun nasarar kubutar da akalla mutane 21 daga hannun 'yan ta'addan.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da rundunar ta bakin jami'in hulda da jama'a da yada labarai na rundunarya fitar a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel