Gwamnoni basu da hujja na kin biyan albashi mafi karanci – Shugaban kungiyar kwadago

Gwamnoni basu da hujja na kin biyan albashi mafi karanci – Shugaban kungiyar kwadago

- Shugaban kungiyar kwadago, Boboi Kaigama ya bayyana cewa gwamnatocin jiha basu da wani hujja nakin kara albashin ma’aikata mafi karanci

- Kaigama na neman takaran kujerar gwamnan jihar Taraba karkashin APC

- Yace karin albashin karshe da akayi ya kasance lokacin da dalai ke kan N150

Shugaban kungiyar kwadago, Boboi Kaigama wadda ke takaran kujerar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana cewa gwamnatocin jiha basu da wani hujja nakin kara albashin ma’aikata mafi karanci.

Ya bayyana hakan jim kadan bayan ya yanki fam dinsa na takara a sakatariyar APC na kasa dake Abuja, a ranar Juma’a, 7 ga watan Satumba.

Gwamnoni basu da hujja na kin biyan albashi mafi karanci – Shugaban kungiyar kwadago

Gwamnoni basu da hujja na kin biyan albashi mafi karanci – Shugaban kungiyar kwadago
Source: Depositphotos

Kaigama yace abun kaico ne a wannan lokaci ganin gwamnatocin jiha suna nokewa lokcin da ake kokarin ganin an fara biyan N66,000 a matsayin mafi karancin albashi da kumgiyar kwadago ta shirya.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ina neman kujerar Buhari ne domin na hada kan Najeriya - Saraki

A cewarsa, mambobin kungiyar kwadago a fadin Najeriya na kokarin ganin sun cimma burinsu, cewa da gangan wasu gwamnoni ke haddasa rikici a yankunansu don su hamdame kudade ta hanyar amfani da harkar tsaro a matsayi maboya.

Kaigama yace lamarin Karin albashi ne hakki ne na ma’aikatan Najeriya. Yace karin albashin karshe da akayi ya kasance lokacin da dalai ke kan N150. Yanzu kuma ya ninka haka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel