Kamar yadda aka yi a Ingila, za'a daina cutar Kwalara a Najeriya

Kamar yadda aka yi a Ingila, za'a daina cutar Kwalara a Najeriya

- Za a kawo karshen barkewar ciwon kwalera a cikin shekaru biyar masu zuwa

- Naira tiriliyan 6.071 aka ware don habaka bangaren lafiya

- Tsarin zai hada da duk jihohi 36 ne tare da birnin tarayya

Kamar yadda aka yi a Ingila, za'a daina cutar Kwalara a Najeriya

Kamar yadda aka yi a Ingila, za'a daina cutar Kwalara a Najeriya
Source: Depositphotos

Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf don kawo karshen barkewar kwalera a fadin kasar nan a shekaru 5 masu zuwa

Ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya bayyana hakan bayan taron FEC da sukayi da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Kamar yanda yace, daga cikin yunkurin da sukayi ya hada da : gyaran bangaren samar da ruwa da kuma wayar da kai a bangaren lafiya.

DUBA WANNAN: Bianca Ojukwu ta rasa takara

Ministan yace Naira tiriliyan 6.071 aka ware don habaka bangaren lafiya. Tsarin kuma zai hada da jihohi 36 na kasar nan tare da babban birnin tarayya, Abuja.

Adewole ya bayyana cewa tsarin farkon ya fara ne daga 2010 zuwa 2015 wanda manufofin su biyu kacal aka cimma wa a cikin 52.

Wannan tsarin kuwa zai fara ne daga 2018 zuwa 2022 wanda ake fatan ya kawo karshen barkewar cutar kwalera a duk fadin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel