An gurfanar da wani 'Dan 'Kwallo bisa laifin satar Dukiya a Coci

An gurfanar da wani 'Dan 'Kwallo bisa laifin satar Dukiya a Coci

Wani dan wasan kwallon kafa, Sola Fabiyi, ya gurfana a gaban kotun majistire dake zamanta a birnin Ikeja, bisa laifi irin dan hali na satar dukiya har ta kimanin N320, 000 a wani babban Coci dake unguwar Alagbado ta jihar Legas.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, ana zargin Sola da aikata laifi irin na dan bera, inda jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu, Sufeto Victor Eruada, ya shaidawa kotun cewa ya aikata wannan laifi ne da misalin karfe 6.00 na safiyar ranar 18 ga watan Agustan da ya gabata.

Sufeto Victor ya ci gaba da cewa, Sola tare da wasu masu hannu cikin wannan laifin sun yashe dukiyar wani Coci ta kimanin N320, 000, inda a halin yanzu shi kadai ne ya shiga hannu sakamakon cin kafar kare da sauran suka yi.

An gurfanar da wani 'Dan 'Kwallo bisa laifin satar Dukiya a Coci

An gurfanar da wani 'Dan 'Kwallo bisa laifin satar Dukiya a Coci
Source: Depositphotos

Eruada ya ci gaba da cewa, wannan miyagun mutane sun kuma yi awon gaba da wani Babur mai lambar LAR 537 QJ, wanda suka yi amfani da shi wajen jigilar dukiyar da suka sata a babban Cocin.

Kamar yadda jami'in dan sandan ya bayyana, Legit.ng ta fahimci cewa wannan laifi yana cin karo da sassa na 287, 311 da kuma 411 cikin kundin tsarin dokoki na jihar Legas.

KARANTA KUMA: Kungiyar Ma'aikatan Man Fetur ta shiga yajin aiki a jihar Delta

Kazalika kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, bisa ga tanadi na kundin tsarin dokokin na jihar Legas, hukuncin wannan laifi kamar yadda dokar ta shar'anta bai wuci shekaru uku a gidan kaso ba ga duk wanda ya aikata.

Sai dai alkaliyar kotun, Mrs M. I. Dan-Oni, ta bayar da belinsa akan zunzurutun kudi na N300, 000 tare da daga sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Satumba domin ci gaba da shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel