Jam'iyyar APC ta kara wa'addin sayar da fam din takara

Jam'iyyar APC ta kara wa'addin sayar da fam din takara

- Jam'iyyar APC ta kara wa'addin sayarwa da mayar da fam din takara

- Jam'iyyar ta sanar da karin wa'addin kwana daya daga ranar 10 ga watan Satumba zuwa 11 ga watan na Satumba

Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta ce ta kara wa'addin kule sayarwa da mayar da fam din takara a kujerun shugaban kasa, gwamnoni, 'yan majalisun dattawa da na wakilai zuwa ranar Talata, 11 ga watan Satumban 2018.

Jam'iyyar APC ta kara wa'addin sayar da fam din takara

Jam'iyyar APC ta kara wa'addin sayar da fam din takara
Source: Twitter

A baya jam'iyyar za ta kulle sayarwa da karbar fam din ne a ranar 10 ga watan Satumban 2018.

DUBA WANNAN: Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi

Mun samu wannan bayanin ne cikin wata sanarwa da mukadashin sakataren yada labarai na jam'iyyar, Yekini Nabena ya aikewa Legit.ng.

Dukkan masu neman takarar kujerun da aka lissafa za su mayar da cikakun fam dinsu zuwa sakatariyar jam'iyyar na kasa ko jiha kafin tashi aiki a ranar 11 ga watan na Satumba.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa jam'iyyar ta umurci wadanda suka gaza siyan fam din a jihohinsu su garzaya zuwa ofishin jam'iyyar da ke babban birnin tarayya Abuja domin sayan fam din.

A sanarwan da ta fito daga bakin mukadashin sakataren yada labaran jam'iyyar, Yekini Nabena, ta ce jam'iyyar ta samu korafin cewa wasu masu son siyan tikitin takaran basu samu ikon saya a jihohinsu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel