Kada ku sauya sheka idan kun fadi zaben fitar da gwani - PDP a Bauchi ta roki yan takara

Kada ku sauya sheka idan kun fadi zaben fitar da gwani - PDP a Bauchi ta roki yan takara

- Jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Bauchi ta roki yan takara karkashin jam'iyyar da kada su sauya sheka ko da sun fadi a zaben fitar da gwani

- Shugaban jam'iyyar na jihar, ya ce jam'iyyar zata gudanar da sahihin zabe da yin adalci ga kowa, don samar da nagartattun yan takara a matakan shugabanci daban daban

- Hukumar INEC, ta tsara jadawalin ranakun da jam'iyyu zasu gudanar da zaben fitar da gwani, daga ranar 20 ga watan Satumba zuwa 06 ga watan Oktoba, 2018

Jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Bauchi ta roki yan takara karkashin jam'iyyar da kada su sauya sheka daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun ko da sun fadi a zaben fitar da gwani.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Alhaji Hamza Akoshe Akuyam ya yi wannan rokon a lokacin da wani dan majalisar wakilai ta tarayya, mai wakiltar mazabar Toro, Joshua Titus Sanga, ya maida fom din nuna sha'awar tsayawa takara karkashin jam'iyyar, a sakatariyar jam'iyyar da ke Bauchi.

Shugaban jam'iyyar wanda ya samu wakilcin shugaban matasa na jam'iyyar, Murtala Abubakar ya ce akwai bukatar yan takarar su ci gaba da kasancewa a cikin jam'iyyar ba tare da komawa wata ba, ko da ba su samu nasara a zaben fitar da gwani ba, don yin aiki tare da nufin samun nasarar jam'iyyar a babban zabe na 2019.

Ya jaddadawa yan takara cewa jam'iyyar zata gudanar da sahihin zabe da yin adalci ga kowa, don samar da nagartattun yan takara a matakan shugabanci daban daban, da zasu iya karawa tare da samun nasara akan sauran yan takara daga sauran jam'iyyu.

KARANTA WANNAN: Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku

Kada ku sauya sheka idan kun fadi zaben fitar da gwani - PDP a Bauchi ta roki yan takara

Kada ku sauya sheka idan kun fadi zaben fitar da gwani - PDP a Bauchi ta roki yan takara
Source: Depositphotos

"Muna baiwa dukkanin yan takara da ke neman kujeru daban daban karkashin jam'iyyar PDP da su sani cewa za'a gudanar da sahihin zaben fitar da gwani. Don haka zai zama kamar butulci ga duk dan takarar da ya fadi a zaben ya ce zai koma wata jam'iyyar. Ya kamata a ce an hada kai bayan zaben don fuskantar babban zabe na 2019." a cewarsa.

A jawabinsa, kodinetan yakin zaben dan takarar, Malam Musa Abubakar, ya shaida cewa dan takarar na da dukkanin siffofin shugabanci da ake bukata don haka ya kamata jam'iyyar ta bashi goyon baya duba da irin ayyukan raya kasa da ya kaddamar a lokacin da ya ke aikin gwamnati.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta tsara jadawalin ranakun da jam'iyyu zasu gudanar da zaben fitar da gwani, daga ranar 20 ga watan Satumba zuwa 06 ga watan Oktoba, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel