Yan sanda sun sha alwashin yin maganin yan daban siyasa da masu daukar nauyinsu a Kano

Yan sanda sun sha alwashin yin maganin yan daban siyasa da masu daukar nauyinsu a Kano

- Yan sanda sun ya alwashin yin maganin yan daban siyasa a Kano

- Sun kuma lashi takobin duk dan siyasa da suka samu da hannun wajen daukar nauyinsu

- Kwamishinan yan sanda n jihar yace siyasa ba abun a mutu ko a rayu bane

Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana jajircewarta na kore yan daban siyasa a jihar kafin zaben 2019.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Malam Rabiu Yusuf ya bayyana hakan a wani ganawa tare da shugabannin jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar.

Kwamishinan wadda ya samu wakilcin mataimakinsa, DCP Balarabe Sule ya jadadda cewa “zamanin da yan siysa ke haddasa rikici su ci lafiya ya wuce”, inda ya kara da cewa rundunar yan sanda a shirye take ta yi maganin duk wani dan siyasa dake daukar nauyin yan daba domin su haddasa tashin hankali a kowani yanki na jihar.

Yan sanda sun ya alwashin yin maganin yan daban siyasa da masu daukar nauyinsu a Kano

Yan sanda sun ya alwashin yin maganin yan daban siyasa da masu daukar nauyinsu a Kano
Source: Facebook

Yace yan sanda bazata bar kowani kafa ba domin tabbatar da zaman lafiya wajen gudanar da zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: PDP zata sha kan APC da mamaki a 2019 - Bwacha

Ya bukaci shugabannin jam’iyyun siyasa daban-daban da su karya gwiwain yan takaransu daga siyasar dabanci inda ya kara da cewa siyasa ba abun rayu ko a mutu bane.

Ya kuma bukaci yan siyasa das u sanar da yan sanda game da duk wani taron siyasa da zasu yi sa’o’i 48 kafin taron.

Shugabannin jam’iyyu daban-daban da suka halarci taron sun bayyana hakan a matayin abu mai kyau sannan sun yi alkawarin bin tsarin dokar domin ganin anyi zabe cikin kwanciyar hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel