Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

- Kwamiti na musamman da fadar shugaban kasa ta kafa don kwato kayayyakin gwamnati a Abuja, ta mika motoci 19 da ta kwato daga wasu tsofaffin jami'an gwamnati

- Shugaban kwamitin ya ce wannan ya zama izna da gargadi ga dukkanin ma'aikatan gwamnati, daga kauracewa daukar kayan gwamnati don amfani na kashin kai

- Daraktan sashen kidayar jama'a na hukumar ta NPopC, Mr. Liman Baba, ya ce kwato motocin, zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun zirga zirga a hukumar

Kwamiti na musamman da fadar shugaban kasa ta kafa don kwato kayayyakin gwamnati a Abuja, ta mika motoci 19 da ta kwato daga wasu kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa (NPopC), wadanda akai zargin sun yi awon gaba da motocin bayan da wa'adinsu a aikin ya kare.

Shugaban kwamitin, Mr Okoi Obono-Obla, ya mika motocin ga jami'an hukumar bayan da aka gudanar da wani taron murna na musamman.

Obono-Obla ya ce an kwato motocin bayan da kwamitin ya samu kwakkwaran bayani daga wani ma'aikacin hukumar a watan Mayu.

Ya bayyana cewa yadda tsofaffin kwamishinonin suka tafi da motocin ya saba doka, kasancewar kayan gwamnati ne, musamman duba da cewa gwamnati ta tallafa masu ta hanyar wani shiri na basu tallafin kudade.

"Amma kasancewar Nigeria na cike da jami'ai masu cin hanci da rashawa, har sai da wannan gwamnati ta shugaban kasa Buhari ta hau mulki, a gwamnatin baya, jami'ai na tafiya da mocin gwamnati da zaran wa'adinsu na aiki ya kare, wanda hakan ya sabawa doka.

Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe

"Idan da ace har yanzu Nigeria na a lokutan baya, kafin watan 28 ga watan Mayu, 2015, to da wadannan tsofaffin kwamishinonin sun ci bulus akan motocin, wanda hakan zai tauye hakkin wasu yan Nigeria na amfani da su.

"An samar da motocin ne don gudanar da ayyukan hukumar kidaya ta kasa, amma wasu jami'an hukumar marasa kishin kasa suka tafi da su gidajensu. Don haka, sai muka fara bincike daki bayan daki, har muka samu nasarar kwato motcin daga hannun wadannan tsofaffin kwamishinoni", a cewarsa.

Shugaban kwamitin ya ce wannan zai zama izna da gargadi ga dukkanin ma'aikatan gwamnati, wanda ya hada da shi kansa, daga kauracewa daukar kayan gwamnati don amfani na kashin kai.

Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: Daga kallon raini: Dan majalisa ya bukaci kotu ta garkame kakakin majalisar Nasarawa

A yayin da ya ke nuni da cewa kayan gwamnati, mallakin gwamnati ne kawai don amfanin yan Nigeria baki daya, ya ce gwamnatin shugaban kasa Buhari ba zata lamunci irin wannan dabi'a ta daukar kayan jama'a ba.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa, Daraktan sashen kidayar jama'a na hukumar ta NPopC, Mr. Liman Baba, wanda ya karbi motocin a madadin shugaban hukumar, Mr Eze Duruiheoma, ya jinjinawa kwamitin bisa wannan namijin kokari.

Baba ya ce kwato motocin, zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun da hukumar ke fuskanta, musamman ta fuskar zirga zirga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel