Ana saura kimanin kwanaki hamsin da karewar wa’adinsa, Fayose zai sayi motar N75 Million, ma’aikata kuma watanni 8 babu albashi

Ana saura kimanin kwanaki hamsin da karewar wa’adinsa, Fayose zai sayi motar N75 Million, ma’aikata kuma watanni 8 babu albashi

- Gwamna Ayodle Fayose zai kare wa'adinda nan na watanni biyu a matsayin gwamna

- Zai tattara inasa-inasa zai bar sabon gidan gwamnatin da ya gina

- Zai tafi ma'akatan jihar na binsa kudin albashin watanni 8

Ma’aikatan jihar Ektii sun nuna bacin ransu gane da gwamnan jihar, Ayo Fayose, kan sayan mota kirar Lexus na kudi N75 Million a matsayin tsarabar karewar wa’adi ana saura kasa da kwanaki hamsin da karewar wa’adinsa a matsayin gwamnan jihar.

Kana sun caccaki gwamnan kan baiwa kansa da mataimakin, Kolapo Olusola, kudi N43 million a matsayin la’ada.

Kungiyoyin kwadagon jihar ta NLC da TUC sun ce wannan abu da gwamnan yayi rashin hankali ne da kuma rashin tausayin ma’aikatan jihar.

Ana saura kimanin kwanaki hamsin da karewar wa’adinsa, Fayose zai sayi motar N75 Million, ma’aikata kuma watanni 8 babu albashi

Ana saura kimanin kwanaki hamsin da karewar wa’adinsa, Fayose zai sayi motar N75 Million, ma’aikata kuma watanni 8 babu albashi
Source: Depositphotos

Kungiyoyin sun yi mamakin yadda gwamna zai ki biyan bashin albashin ma’aikata amma ya rika siyan manyan motoci da kyautuan kudi daga asusun gwamnati.

Ma’aikatan gwamnati na bin bashin albashin watanni 8 yayinda yan fanshi na bin bashin watanni tara.

KU KARANTA: Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku

A jawabin da kungiyoyin kwadagon suka saki, shugaba kungiyar NLC, Mr Ade Adesanmi da takwararsa na TUC, Mr Odunayo Adesoye, ya siffanta wannan kyauta matsayin son kai.

Sunce kamata yayi Fayise ya mayar da hankali kan yadda zai biya bashin ma’aikata da yan fansho amma yayi burus. Sun lashi takobin cewa idan har aka aiwatar da wannan abu, sai sun tayar da tarzoma a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel