Yanzu Yanzu: Shekarau ya koma APC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar

Yanzu Yanzu: Shekarau ya koma APC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar

- Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

- Shekarau ya sanar da hukuncinsa na komawa jam’iyyar APC mai mulki bayan ganawar sirri da suka yi tare da shugaban jam’iyyar APC na kasa

- Taron ya gudana a jihar Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shekarau ya sanar da hukuncinsa na komawa jam’iyyar APC mai mulki bayan ganawar sirri da suka yi tare da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole.

Yanzu Yanzu: Shekarau ya koma APC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar

Yanzu Yanzu: Shekarau ya koma APC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar
Source: UGC

An gudanar da ganawar sirrin ne a ranar Juma’a, 7 ga watan Satumba a jihar Kano.

Gwamna Abdullahi Ganduje da sauran manyan jami’an jam’iyyar ma su halarci ganawar.

Yanzu Yanzu: Shekarau ya koma APC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar

Yanzu Yanzu: Shekarau ya koma APC bayan ganawa da shugabannin jam’iyyar
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: 2019: Bazan iya cutar da ku ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunku - Saraki ya yiwa APC gugar zana

Shekarau yayinda yake sanar da sauya shekarsa yace yayi imanin cewa akwai bukatar ya sauya shekar duba ga halin da siyasar Najeriya ke ciki, yana matukar muhimanci ya koma APC.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisa, Sanata Emmanuel Bwacha ya bayyana cewa Peoples Democratic Party (PDP), ta kulla yarjejeniya da dukkanin yan takaranta na kujerar shugaban kasa domin tabbatar da ganin ta kori gwamnatin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a 2019.

Bwacha wadda yayi Magana a Jalingo a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba bayan ya mayar da fam dinshi na ra’ayin takaran sanata a sakatariyar PDP dake jihaar Taraba inda ya bayyana cewa PDP zata shayar da APC mamaki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel