Dabaru 7 da za ayi amfani dasu a duk lokacin da girgizan kasa ya faru

Dabaru 7 da za ayi amfani dasu a duk lokacin da girgizan kasa ya faru

Duk da cewa kasar Najeriya ba mai yawan samun mummunar girgizan kasa bace kamar sauran sassan kasashen Duniya, amma anan gida Najeriya akan samu wasu yan kananan girgizan kasa, wand aka iya sanya mutane cikin firgici da rudani.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tun daga ranar Laraba har zuwa Juma’a 7 ga watan Satumba anyi ta samun karamin girgizan kasa a babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan ya firgita mazauna unguwannin Mpape da Maitama sakamakon wannan ne karo na farko da suka fuskanci lamarin.

KU KARANTA: Dawo dawo: Buhari ya roki yan Najeriya dake kasashen waje dasu dawo Najeriya

Sai dai baya da Abuja, an taba samun kwatankwacin wannan girgizan kasar a jihohin Kaduna, Ogun, Bayelsa, Ribas da Oyo, kuma bincike ya nuna irin wannan girgizan na farko a Najeriya ya faru ne a shekarar 1933.

Dabaru 7 da za ayi amfani dasu a duk lokacin da girgizan kasa ya faru

Girgizan
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa kasar China ce kasar dake kan gaba wajen samun girgizan kasa, inda a jimlace girgizan kasa ya kashe sama da mutane dubu dari takwas (800,000) a kasar tun daga shekarar 1900 zuwa 2016.

Haka zalika bincike ya nuna abubuwan dake janyo irin wannan karamin girgizan sune matsawar wasu sinadarai a karkashin kasa, haka zalika ayyukan mutane kamar su fasa duwatsu da nakiya, hakar man fetir, hakar ma’adanan kasa da kuma fashewa makamin nukiliya na iya kawo girgizan.

Sai dai fa binciken yace babu abinda zai iya hana faruwar wannan girgizan, sai dai kawai kwararru a harkar gine gine su dinga kulawa wajen gine gine saboda gidaje ne lomar farko idan lamarin ya faru, amma akwai wasu hanyoyi bakwai da ka iya tseratar da mutum idan girgizan ya faru;

- Kada a firgita, ka natsu ka nemi wajen tsira

- A kashe na’urar iskar gas, da kayan wuta don hana gobara

- A kauce ma wayoyin wutar lantarki, bishiyu da gadoji

- Idan ana cikin daki ne na kwanta da hannuwanka a bayan kanka ka shige karkashin tebur

- A kauce ma dakin girke girke da tagogi don kada girgizan ya jefo maka wuka ko gilashi

- A ajiye wayar salula a kusa a kira lambobin bada agajin gaggawa

- A nemo akwatin magunguna a ajiye a kusa saboda kota kwana

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel