Martani: Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku

Martani: Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lissafa badakalar da ake yi a gwamnatin shugaban kasa Buhari

- A ranar Laraba fadar shugaban kasa ta maida martani kan wani ikirari da Atiku yayi na cewar shugaban kasa Buhari yasha giyar mulki ya bugu

- Sai dai Atiku a cikin wata sanarwa da ya bayar a jiya Alhamis, ya kara jaddada cewa Buhari ya sha giyar mulki ya bugu

Tsohon shugaban kasa kuma wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lissafa abubuwan da ya kira da badakala a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Atiku Abubakar, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP, ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata sanarwa daga fadar shugaban kasa.

A ranar Laraba fadar shugaban kasa ta maida martani kan wani ikirari da Atiku yayi na cewar shugaban kasa Buhari yasha giyar mulki ya bugu, tana mai cewa babu wani abu da zai iya girgiza Buhari, musamman ma yaki da cin hanci da rashawa.

KARANTA WANNAN: Bayan shekaru 48: A karon farko Mace ta zama shugabar ma'aikata jihar Benue

Sai dai Atiku a cikin wata sanarwa da ya bayar a jiya Alhamis, ya kara jaddada cewa Buhari ya sha giyar mulki ya bugu, tare da lissafo wasu badakaloli da ake yi a karkashin gwamnati mai ci a yanzu.

Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku

Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku
Source: Facebook

Ya ce: "Idan har har martanin da suka mayar gaskiya ne, na cewar giyar mulki bata bugar da Buhari ba, to me ya sa fadar shugaban kasa ta ki daukar mataki a lokacin da Antoni Janar na kasar, Abubakar Malami, ya je kotu tare da kitsa tuggun hana majalisar dattijai yin bincike akan karin matsayin da akayi Abdulrasheed Maina har sau biyu a lokaci daya?

"Idan har ta tabbata shugaban kasa Buhari bai karkace akan alkawuran da ya dauka ba a zaben 2015, to ya akayi har hukumar kiddiddigar cin hanci da rashawa ta kasa da kasa ta bayyana Nigeria a matsayin kasar da cin hanci yayi mata katutu fiye da shekarar 2015, sabanin yadda yayi karanci a mulkin PDP?

"Baya ga haka, muna tambayar ta yadda akayi shugaban kasar ya zamo kaifi daya bayan kowa ya na ganin ministar da ake zargi da buga takardar shaidar yin bautar kasa ta bogi ta na ci gaba da zama a kan mukaminta. Shin wannan adalci ne ko yaudara, ko cin hanci?" Don haka sai Atiku ya ce Buhari na zagaye da hadiman da ke fada masa karya don neman tagomashi.

KARANTA WANNAN: An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe

Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku

Giyar mulki ce ta makantar da Buhari daga ganin tarin badakalar da ake yi a gwamnatinsa - Atiku
Source: Depositphotos

"Ta bayyana karara cewa shugaban kasa na zagaye da mutanen da burinsu kawai su wawuri dukiyar al'umma ta hanyar lullube gaskiya da karya, irin mutanen da ke fadi masa abunda ya ke so ya ji, idan ba haka ba, babu yadda za ayi a kira gwamnatin da ta kara farashin mai, a lokaci daya tana biyan kudin tallafi kamar yadda ta ke biya a baya, a ce a kirata da gwamnati mai yaki da cin hanci da rashawa

"Ya kamata jama'a su hankalta da cewa idan har farashin mai ya karu da kashi 68, daga N87 akan kowace lita, zuwa N145, to ya zama wajibi kudin da gwamnati ta ke biya na tallafin mai ya ragu, musamman ganin cewa farashin danyen mai ya ragu." a cewar Atiku.

Sai dai dan takarar shugaban kasar, ya yi wani lissafi, wanda ya ce gwamnatin Buhari na biyan ministan cikin gida kan harkokin man fetur, zambar Naira miliyan N1.4 a matsayin kudin tallafin mai a kowace shekara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel