Yanzu-yanzu: Kano ta cika da shewa yayinda Oshiomole da Ganduje suka dira gidan Shekarau (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Kano ta cika da shewa yayinda Oshiomole da Ganduje suka dira gidan Shekarau (Bidiyo)

Labarin da shigowa yanzun nan na nuna cewa shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC, Kwamred Adams Oshiomole, da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun dira gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Mun kawo muku rahoton cewa ganawar na daga cikin shirye-shirye da yarjejeniya kafin sauya shekar Shekarau gobe Asabar, 8 ga watan Satumba, 2018.

An shirya zaman ne domi kara gamsar da Sardaunan Kanon muhimmanci fitarsa daga PDP.

Mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya bayyana a daren jiya cewa tsohon gwamnan zai yanke shawararsa na tsayawa ko fita daga PDP ranan Asabar.

Kana mai magana da yawun gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakassai ya jaddada hakan a wani jawabi da yayi a shafinsa na Tuwita.

Kalli Bidiyon:

KU KARANTA: 2019: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel