PDP zata sha kan APC da mamaki a 2019 - Bwacha

PDP zata sha kan APC da mamaki a 2019 - Bwacha

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisa, Sanata Emmanuel Bwacha ya bayyana cewa Peoples Democratic Party (PDP), ta kulla yarjejeniya da dukkanin yan takaranta na kujerar shugaban kasa domin tabbatar da ganin ta kori gwamnatin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a 2019.

Bwacha wadda yayi Magana a Jalingo a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba bayan ya mayar da fam dinshi na ra’ayin takaran sanata a sakatariyar PDP dake jihaar Taraba inda ya bayyana cewa PDP zata shayar da APC mamaki.

Yace: “Mun kulla yarjejeniyar fahimta tsakanin dukkanin yan takaran kujerar shugaban kasa cewa duk wadda ya zamo zakara zai tafi da sauran.

PDP zata sha kan APC da mamaki a 2019 - Bwacha

PDP zata sha kan APC da mamaki a 2019 - Bwacha
Source: Depositphotos

“Mun shirya sosai don kwace gwamnati daga hannun APC sannan kuma baza muyi sanya ba.”

A cewarsa jam’iyyar PDP na da haddin kai fiye da na kowani lokaci tare da takardun da suka kamata.

KU KARANTA KUMA: An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe

A halin da ake ciki, a kokarin gujema yiwuwar afkuwar rikici bayan zaben fidda gwaninta na yan takaran shugaban kasar ta, kwamitin amintattu na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Walid Jibrin ya bayyana cewa kwamitin na duba ga yiwuwar rage yawan yan takaranta na shugaban kasa.

Mista Jibrin ya bayyana haakan a Abuja a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba bayan wata ganawa tare da mambobin kwamitin amintattun.

Zuwa yanzu dai jam’iyyar PDP na da yan takara 13 dake neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel