An sami qarin masu dangwala zabe da miliyoyi a 2019 - INEC

An sami qarin masu dangwala zabe da miliyoyi a 2019 - INEC

- Katin zabe na dindindin 16,500,192 zamu kammala kafin zaben 2019

- A cikin wata goma sha shida, munyi ma mutane 14,551,482

- Jimillar wadanda ke da katin zabe sune 84,271,832

An sami qarin masu dangwala zabe da miliyoyi a 2019 - INEC

An sami qarin masu dangwala zabe da miliyoyi a 2019 - INEC
Source: Depositphotos

Hukumar zabe mai zaman kanta, tace zata buga katin zabe na dindindin guda 16,500,192 kuma zata raba su ga masu shi kafin zaben 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a taron shi da REC a ranar Alhamis, da ya gudana a Abuja.

Yakubu yace, cikin watanni 16,anyi wa 14,551,482 sababbin katunan zabe a fadin kasar. Idan aka hada su da 69,720,350 da suke da katunan zabe, zai kama 84,271,832 kenan.

Yayi bayanin cewa za a iya samun kasa da haka domin har yanzu ba a tentacle ba.

Kari akan sababbin rijista, hukumar tana aiki akan 769,917 katunan dake so a canza musu jihar ko gurin zabe, 1,178,793 wadanda katunan su ya bace ko ya lalace, tare da gyara akan bayanan dake kan katin.

DUBA WANNAN: An fille kan dansanda a Jos

A halin yanzu hukumar ta fitar da katunan dindindin ga wadanda sukayi rijista a 2017 kuma an kaisu guraren da za a karba.

Ya tabbatar da cewa an buga katunan da akayi rijista a farkon 2018,kuma za a kaisu jihohin su a mako mai kamawa.

Muna tabbatar ma duk Dan Najeriya da yayi rijista katin zabe, zai samu katin shi na dindindin kafin zuwan zaben 2019. Zamu saukake hanyar karbar katin zaben, har zuwa ana saura sati daya zaben ne zamu tsaya, inji Yakubu

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel