Qauyen su Ojukwu sun 'kori' matarsa Bianca, sunce baza su bata takarar sanata ba

Qauyen su Ojukwu sun 'kori' matarsa Bianca, sunce baza su bata takarar sanata ba

- Bazamu zabi Bianca ba, saboda ba yar jihar Anambra bace

- Mace ce da bata san matsalolin mu ba

- Dan jihar mu zamu zaba, ba bare ba

Qauyen su Ojukwu sun 'kori' matarsa Bianca, sunce baza su bata takarar sanata ba

Qauyen su Ojukwu sun 'kori' matarsa Bianca, sunce baza su bata takarar sanata ba
Source: Depositphotos

Iyalan marigayi Chief Odumegwu Ojukwu sunyi alkawarin bazasu goyi bayan matar shugaban inyamurai ba, Bianca, koda kuwa taci zaben fidda gwani na APGA, a zaben 2019 dake kusantowa.

Kamar yanda suka ce, Bianca ba yar asalin jihar Anambra bace, kuma bazata iya mulkar yan kudancin jihar ba.

Sunce matar yar asalin Ngwo ce, jihar Enugu, kuma zata iya kara aure ko a gobe ne.

Dr Ike, daya daga cikin daraktocin Ojukwu Transport Company limited, yace bai dace ba su zuba ido, mace daga Ngwo ta mulke su.

"Munfi son Dan asalin garin mu ya mulke mu. Wannan matar ta auri marigayi mahaifin mu, kuma daga Enugu take. Zata iya aure a koda yaushe, Dan jihar Abia ko ma Dan jihar Sokoto. Babu inda aure ba zai iya kaita ba." inji su.

DUBA WANNAN: An fille kan dansanda a Jos

Majiyar mu ta sanar mana yanda Bianca, ta shiga jerin manema kujerar sanatan Anambra ta kudu karkashin APGA.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel