Dalilin da ya sanya 'Yan Najeriya ba za su amince da David Mark a matsayin Shugaban kasa ba - Tsohon Shugaban 'Daliban Najeriya

Dalilin da ya sanya 'Yan Najeriya ba za su amince da David Mark a matsayin Shugaban kasa ba - Tsohon Shugaban 'Daliban Najeriya

A ranar Alhamis din da ta gabata ne tsohon shugaban kungiyar dalibai ta Najeriya kuma manemin takarar kujerar sanatan jihar Benuwe ta Kudu, Daniel Onjeh, ya kirayi al'ummar Najeriya akan su fita batu na kudirin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, na neman kujerar shugabancin kasar nan.

Onjeh ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan mallakar fam dinsa na takara cikin babban birnin kasar nan na Abuja.

Tsohon shugaban daliban ya bayyanawa manema labarai cewa, al'ummar kasar nan su fita batun David Mark dangane da kudirin sa na neman kujerar shugabancin kasar nan da cewar ba Mutumin da za a dogara da shi ba ne ta fuskar yarda ko aminci.

David Mark yayin mallakar fam dinsa na takara a ofishin jam'iyyar PDP

David Mark yayin mallakar fam dinsa na takara a ofishin jam'iyyar PDP
Source: Original

Mista Onjeh yake cewa, tsohon shugaban Majalisar dattawan ba ya da wata cancanta ko ta sisi kobo ta jagorantar kasar nan sakamakon gazawarsa da ta bayyana karara yayin da ya jagorancin majalisar ta dattawa shekaru kadan da suka gabata.

KARANTA KUMA: Sai Kotu ta tsame hannun ta daga dambarwar tsige Saraki - Ministan Shari'a

Ya ci gaba da cewa, bayan tsawon shekaru da ya shafe a kan kujera ta shugabancin majalisar dattawa, ba bu wani abun zo a gani da David Mark ya tsinanawa mazabar sa da al'ummar jihar Benuwe ta Kudu.

Kazalika Mista Onjeh ya hikaito yadda tsohon shugaban majalisar ya datse masu dukkan wani jin dadi na sharbar romon dimokuradiyya ta fuskar rashin ci gaba na gine-gine, rashin tsaro gami da kangin talauci da ya jefa su ciki baya ga alkawurra da ya dauka na tabbatuwar hakan a mazabar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel