Bayan shekaru 48: A karon farko Mace ta zama shugabar ma'aikata jihar Benue

Bayan shekaru 48: A karon farko Mace ta zama shugabar ma'aikata jihar Benue

- Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya nada Mrs. Veronica Onyeke, a matsayin sabuwar shugabar ma'aikatan jihar

- An haifi Mrs. Veronica a karamar hukumar Ogbadibo da ke a jihar, kafin wannan nadi nata, ita ce babbar sakatariya a ofishin mataimakin gwamnan jihar

- A yanzu, Onyeke ta dauki kambu na zamowa mace ta farko da aka baiwa mukamin shugabancin ma'aikatan jihar, tun bayan shekaru 42 da kafuwar jihar

A kokarin sa na ganin cewa an yi adalci a rabon mukaman gwamnati, ba tare da nuna wariyar jinsi ba, Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya nada Mrs. Veronica Onyeke, a matsayin sabuwar shugabar ma'aikatan jihar.

Biyo bayan wannan sanarwa ta nadin Onyeke, hakan yasa ta zamo mace ta farko da gwamnatin jihar ta taba nadawa a matsayin shugabar ma'aikatan jihar.

An haifi Mrs. Veronica a karamar hukumar Ogbadibo da ke a jihar, kafin bata mukamin shugabar ma'aikatan jihar, ita ce babbar sakatariya a ofishin mataimakin gwamnan jihar.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren watsa labaransa, Terver Akase, ya yi nuni da cewar sabuwar HOS zata maye gurbin Injiniya George Ede wanda yake shirin yin ritaya.

KARANTA WANNAN: Kowa ya sani: Yan siyasa ne manya manyan makiyan Nigeria - Ango Abdullahi

A karon farko: Mace ta zama shugabar ma'aika a jihar Benue

A karon farko: Mace ta zama shugabar ma'aika a jihar Benue
Source: Original

A yanzu, Onyeke ta dauki kambu na zamowa mace ta farko da aka baiwa mukamin shugabancin ma'aikatan jihar, tun bayan shekaru 42 da kafuwar jihar.

A wani labarin:

Legit.ng ta ruwaito maku cewa, a ranar asabar data gabata ne akalla ma'aikatan jihar Benue 4,000 ne suka zana jarabawar karin matsayi a Makurdi, babban birnin jiahr.

Babban Sakatare a ma'aikatar 'Bureau of Establishment', Mr. Ode Echele, ya bayyana hakan ga manema labarai a Makurdi.

Echele ya ce ma'aikatan da suka zauna jarabawar a ranar asabar, 27 ga watan Augusta, suna a matakin aiki na 6 da wadanda ke sama da hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel