Lawal ya marawa Buhari baya akan kin sanya hannu a kudirin gyara dokar zabe

Lawal ya marawa Buhari baya akan kin sanya hannu a kudirin gyara dokar zabe

Shugaban masu rinjaye a mjalisar dattawa, Dr. Ahmed Laan ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ikon da kujerarsa ta mallaka masa ne da kuma abunda doka ta gindaya na kin sanya hannu a kudirin gyara dokar zabe na 2018.

Lawan wadda ke amsa tambayoyi daga manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) babin jihar Yobe a gidan gwamnati, Damaturu, yace ya zama dole kada a sanya kimiya cikin zabe.

Sanatan yayinda yake ganin laifin majalisar dokoki na aika takardun da bai cika ga shugaban kasar ba sannan suke sa ran ya sanya hannu a kai, ya bayyana cewa Buhari ne shugaban kasar da ya sanya hannu a dokoki mafi yawa a tarihin Najeriya tun bayan da ya hau kujerar mulki.

Lawal ya marawa Buhari baya akan kin sanya hannu a kudirin gyara dokar zabe

Lawal ya marawa Buhari baya akan kin sanya hannu a kudirin gyara dokar zabe
Source: Depositphotos

A halin da ake ciki, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta bayyana ikirarin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cewa gwamnonin APC shida da wasu sanatoci sun kammala shirin komawa jam’iyyarsu a matsayin zaucewa.

KU KARANTA KUMA: An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe

Babban sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Yekini Nabena ya bayyana hakan a wata sanarwa day a fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba a Abuja.

Ya bayyana cewa da wannan ikirari na PDP, ya nuna karara cewa jam’iyyar ta fara taka matsayin shan kayan maye gabannin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel