Babu tsunstu ba tarko: Saraki da su Kwankwaso za su iya yin babban rashi a zaben 2019

Babu tsunstu ba tarko: Saraki da su Kwankwaso za su iya yin babban rashi a zaben 2019

Yayin da ake shirin zaben fitar-da-gwani na 2019, wasu sun fara fahimtar cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da wasu manyan ‘yan siyasan kasar za su iya yin biyu-babu a zabe mai zuwa.

Saraki, Kwankwaso, David Mark, Jonag Jang da Tambuwal za su iya rasa tsuntsu da tarko a 2019 idan ba su raba kafa ba a zaben 2019.

Babu tsunstu ba tarko: Saraki da su Kwankwaso za su iya yin babban rashi a zaben 2019

Atiku, Sule, Kwankwaso su na neman Shugaban kasa a 2019
Source: Twitter

Da-dama daga cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP su na rike da wani mukamin dabam, hakan ke nuna cewa wasu ‘yan siyasa za su rasa mukaman su wajen takakar Shugaban kasa idan ba su raba kafa ba.

Irin su David Mark, Jonah Jang, da Rabiu Kwankwaso duk Sanatocin kasar nan ne da kuma ke neman kujerar Shugaban kasa a 2019 a karkashin PDP. Ganin cewa mutum 1 kurum zai iya samun tikiti, da-dama za su ciza yatsa a lokacin da aka gama zabe.

Cikin ‘yan takarar na PDP akwai wadanda ba su rike da wani mukami kamar su Atiku Abubakar, Sule Lamido, Ahmad Makarfi, Tanimu Turaki da sauran su. Su dai wadannan ba za su rasa komai ba ko da sun sha kasa a zaben fitar da gwanin da za ayi.

KU KARANTA: Kwankwaso ya shiryawa takarar 2019 a Jam'iyyar PDP

Haka kuma Gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo wanda wa’adin sa zai kare a 2019, yana cikin masu neman takara a 2019. Da zarar dai ‘yan siyasa irin su Gwamnan Sokoto sun yi gigin neman Shugaban kasa a PDP, za su rasa mukaman da su ke kai.

Za a fara yin zaben fitar da gwani na Sanatoci ne a PDP kafin ayi na Shugaban kasa. Irin su Saraki za su tafi neman Shugaban kasa wanda babu tabbacin samun nasara domin za su iya shan kasa a zaben, idan aka yi haka dai sun tashi ba-wan-ba-wan kenan.

Jiya ku ka ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya samu hada-kan manyan ‘Yan siyasar da su kayi takarar fitar da gwani na Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai Ademola Adeleke da Akin Ogunbiyi sun amince su yi aiki tare a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel