Daga karshe APC ta bayyana dalilin da yasa fam dinta na takara yayi tsada

Daga karshe APC ta bayyana dalilin da yasa fam dinta na takara yayi tsada

- Akwai barazana daga daga jam’iyyar APC akan gwamnoninta cewa tana iya soke zaben fidda gwani na wakilai da suka nema

- Jam’iyyar APC ta bayyana cewa hakan na iya kasancewa idan har aka samu zanga-zanga daga yan takara game da tsarin da za’ayi amfani dashi a zaben fidda gwani mai zuwa

- Ta kuma bayyana cewa kin amincewa da zaben kato-bayan-kato da gwamnonin suka yi shine ya haifar da tsadar fam din takaran

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba tayi barazana ga gwamnoninta dake neman ayi amfani da zaben fidda gwani ta hanyar amfani da wakilai cewa idan dai aka samu zanga-zanga daga masu ruwa da tsaki ko yan takara, toh babu shakka za’a soke tsarin zuwa zaben fidda gwani na kato-bayan-kato.

Vanguard ta ruwaito cewa tsadar da aka sanya akan fam din takaran jam’iyyar ya kasance saboda kin amincewa da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato da gwamnnin suka yi.

Daga karshe APC ta bayyana dalilin da yasa fam dinta na takara yayi tsada

Daga karshe APC ta bayyana dalilin da yasa fam dinta na takara yayi tsada
Source: Depositphotos

Gwamnonin sakamakon kin amincewa da rokonsu na amfani da wakilai a zaben fidda gwani, sun yanke shawarar kin daukar nauyin zaben fidda gwani na kato-bayan-kato. Hakan ya tursasa sakatariyar APC na kasa tattara kudinta ta hanyar siyar da fam domin daukar nauyin tsarin zaben kato-bayan-kato.

KU KARANTA KUMA: Oshiomole, Tinubu, Ganduje za su gana da Shekarau a yau gabanin sauya shekarsa gobe

A halin da ake ciki, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta bayyana ikirarin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cewa gwamnonin APC shida da wasu sanatoci sun kammala shirin komawa jam’iyyarsu a matsayin zaucewa.

Babban sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Yekini Nabena ya bayyana hakan a wata sanarwa day a fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba a Abuja.

Ya bayyana cewa da wannan ikirari na PDP, “ya nuna karara cewa wajm’iyyar ta fara taka matsayin shan kayan maye gabannin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel