Daga kallon raini: Dan majalisa ya bukaci kotu ta garkame kakakin majalisar Nasarawa

Daga kallon raini: Dan majalisa ya bukaci kotu ta garkame kakakin majalisar Nasarawa

- Mr. Makpa Malla, mai wakiltar Wamba a majalisar dokoki ta jihar Nasarawa ya bukaci kotu da ta garkame kakakin majalisar dokoki ta jihar

- Malla ya ce duk da umurnin da kotu ta bayar na dakatar da majalisar daga kiran kujerarsa wofi, hakan bai hana kakakin majalisar bijirewa umurnun kotun ba

- Da aka tuntube shi, lauyan mai kare kakakin majalisar dokoki ta jihar, Rikki Danlami, ya ce ba zai ce uffan akan wannan batu ba.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Wamba a majalisar dokoki ta jihar Nasarawa, Mr. Makpa Malla, ya bukaci kotu da ta garkame kakakin majalisar dokoki ta jihar, bisa zarginsa da yiwa hukuncin kotu kallon hadarin kaji.

Malla ya yi ikirarin cewa kakakin majalisar ya biijirewa umurnin kotu, bayan da ya kira kujerarsa wofi a majalisar, a ranar 29 ga watan Augusta, sakamakon sauya shekar da ya yi daga APC zuwa APGA.

Malla ya ce duk da umurnin da kotu ta bayar na dakatar da majalisar daga kiran kujerarsa wofi, hakan bai hana kakakin majalisar bayyana kujerarsa da cewar babu kowa a kanta ba.

Daga kallon raini: Dan majalisa ya bukaci kotu ta garkame kakakin majalisar Nasarawa

Daga kallon raini: Dan majalisa ya bukaci kotu ta garkame kakakin majalisar Nasarawa
Source: Facebook

Lauyan da ke kare Malla, Benjamin Davou, ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis, a garin Lafia cewa mai shari'a, Justice Simon Aboki, ya bayar da dokar hana majalisar ayyana kujerar Malla a matsayin wofi a ranar 28 ga watan Augusta.

Ya ce bayyana cewa duk da wannan doka da kotu ta bayar, a ranar 29 ga watan Augusta, majalisar ta yi karan tsayewa dokar, inda ta ayyana kujerar wanda ya karewa a matsayin ba kowa a kanta.

Da aka tuntube shi, lauyan mai kare kakakin majalisar dokoki ta jihar, Rikki Danlami, ya ce ba zai ce uffan akan wannan batu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel