Sauya shekar gwamnoni 6: PDP ta fara zaucewa – Inji APC

Sauya shekar gwamnoni 6: PDP ta fara zaucewa – Inji APC

- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi ma PDP wakin babban bargo

- Tace jam'iyyar adawan ta fara zaucewa gabannin zaben 2019

- Hakan ya biyo bayan ikirarin da jam'iyyar PDP tayi na cewa gwamnonin APC da wasu sanatoci na shirin sauya sheka

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta bayyana ikirarin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cewa gwamnonin APC shida da wasu sanatoci sun kammala shirin komawa jam’iyyarsu a matsayin zaucewa.

Babban sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Yekini Nabena ya bayyana hakan a wata sanarwa day a fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba a Abuja.

Ya bayyana cewa da wannan ikirari na PDP, “ya nuna karara cewa wajm’iyyar ta fara taka matsayin shan kayan maye gabannin zaben 2019.

Sauya shekar gwamnoni 6: PDP ta fara zaucewa – Inji APC

Sauya shekar gwamnoni 6: PDP ta fara zaucewa – Inji APC
Source: Facebook

“Yan Najeriya sun yi watsi da PDP sannan kuma cewa babu abunda take wakilta face – rashawa, rashin gaskiya, lalaci da kuma kwadayi.”

KU KARANTA KUMA: Kowa ya sani: Yan siyasa ne manya manyan makiyan Nigeria - Ango Abdullahi

Nabena ya kara da cewa domin kunyan fuskantar rashin nasara a 2019, PDP ta zabi boyewa bayan karya domin ta boye fuskarta.

Ya bayyana cewa yayinda PDP ta fara zaucewa akan sauya shekar mambobin APC zuwa jam’iyyarta, APC na shirin yadda zata fuskanci zaben 2019 a matsayinta na mai wayo, mai hadin kai kuma mai tattare da karfafan yan siyasa.

Ya bayyana cewa yayinda PDP ke hargagi cikin ciwo, gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da hankali wajen inganta rayuwan yan Najeriya da magance abubuwan da ake bukata wajen habbaka tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel