Mukarraban Buhari ba su san aikin Gwamnati ba – Shugaban Majalisa Saraki

Mukarraban Buhari ba su san aikin Gwamnati ba – Shugaban Majalisa Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi bayanin abin da ya hada Majalisar Tarayya sa-in-sa da Fadar Shugaban kasa. Saraki yayi wannan bayani ne lokacin da ya kai ziyara Jihar Ebonyi.

Mukarraban Buhari ba su san aikin Gwamnati ba – Shugaban Majalisa Saraki

Saraki yace rashin sanin aiki na damun Majalisar Buhari
Source: Depositphotos

A yawon da ‘Dan takarar Shugaban kasa na PDP Bukola Saraki yake yi, ya leka fadar Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi inda ya gana da manyan PDP na Yankin. Saraki ya bayyana cewa rashin sanin aiki ne matsalar Gwamnatin Buhari.

Dr. Bukola Saraki ya bayyana cewa matsalar Majalisa da Shugaban kasa ta fara ne daga rashin kwarewar manyan mukarraban Shugaban Kasa wajen aiki. Saraki yace Majalisar Ministocin Buhari ba ta da ilmin aiki a Gwamnatin Tarayya.

KU KARANTA: Wani babban 'Dan Adawa ya gamu da ajalin sa a Najeriya

Bukola Saraki ya nuna cewa dole ne a samu hadin kai tsakanin bangaren zartarwa na fadar Shugaban kasa da kuma Majalisar Tarayya masu yin dokoki. Saraki yace dole a haka ake tafiya tare da juna idan ana so abubuwa su yi kyau a Gwamnati.

Gwamnan na Ebonyi Injiniya David Umahi ya yabawa Sanata Saraki wanda yayi Gwamna na shekaru 8 a Jihar Kwara kafin ya zo Majalisa har ya samu shugabanci. Saraki ya gana da manyan PDP a Jihar har da tsohon Gwamna Sam Egwu.

Duk a makon nan dai Bukola Saraki ya bayyana dalilin da ya sa yake neman Shugaban kasa a lokacin da yake neman goyon bayan ‘Yan PDP a Kudu maso Gabas. Saraki yace an raba kan ‘Yan Najeriya kwarai da gaske a Gwamnatin nan ta Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel