Sai Kotu ta tsame hannun ta daga dambarwar tsige Saraki - Ministan Shari'a

Sai Kotu ta tsame hannun ta daga dambarwar tsige Saraki - Ministan Shari'a

Mun samu cewa Ministan Shari'a kuma lauyan kolu na kasa, Abubakar Malami, ya murza gashin baki tare da daga gira akan tsoma hannun kotun tarayya cikin dambarwa ta hana tsige shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, Ministan ya yi tsitsiye akan kotun da ta yi kakagida wajen karbar korafi na hana tsige shugaban majalisar daga kujerar sa.

A sakamakon guguwar sauyin sheka da ta kada har da shugaban majalisar da ya sauya daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a watan Yulin da ya gabata, Sanatoci da dama sun ci gaba da kai ruwa rana akan yayi murabus ko kuma a tsige shi ta karfin tsiya muddin ya nuna hali irin na Mutanen farko.

Sai dai duk tsanin wannan adawa ga shugaban majalisar bai rasa masoya ba, inda a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata wasu Sanatoci biyu, Isa Misau da kuma Rafiu Adebayo, suka shigar da korafi har gaban kuliya domin sanya hijabi da katanga ta dakile duk wani yunkuri na tsige shugaban majalisar.

Sai Kotu ta tsame hannun ta daga dambarwar tsige Saraki - Ministan Shari'a

Sai Kotu ta tsame hannun ta daga dambarwar tsige Saraki - Ministan Shari'a
Source: Depositphotos

Wannan korafi dake gaban kuliya ya hadar da lauyan kolu na kasa, shugaban majalisar tare da mataimakin sa, shugaba mai rinjaye da maras rinjaye da kuma mataimakansu.

Sauran wanda korafin ya shafa sun hadar da; Magatakardan majalisar da mataimakin sa, sufeto janar na 'yan sanda, shugaban hukumar DSS da sauran kusoshi na majalisar ta dattawa.

A yayin mayar da zance a ranar Alhamis din da ta gabata, Lauyan Ministan Shari'a, Abdullahi Abubakar, ya shaidawa kotun kalubalen dake tukarar ta na sanya hannu tsamo-tsamo cikin dambarwar tsige shugaban majalisar.

KARANTA KUMA: Amfani 10 na Ganyen Mangwaro ga lafiyar 'Dan Adam

Sai dai alkalin kotun, Nnamdi Dimgba, ya bayyana cewa kotun ba za ta saurari duk wani korafi ba har sai zaman sauraro na gaba da za ta gudanar a ranar 19 ga watan Satumba dangane da wannan lamari.

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da jam'iyyar APC ta yi tsayuwar daka kan tsige Saraki ko kuma ya yi murabus salin-alin, jam'iyyar PDP kuma ta ja dunga ta kalubalantar wannan lamari.

A halin yanzu majalisar na ci gaba a gudanar da hutun ta yayin da Saraki ya kasance daya daga 'yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin sabuwar jam'iyyar sa ta PDP domin fafatawa a babban zabe na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel