Muddin APC ta ki sauraran Gwamnonin ta, to za a sha kashi a hannun PDP – Mai ba Buhari shawara

Muddin APC ta ki sauraran Gwamnonin ta, to za a sha kashi a hannun PDP – Mai ba Buhari shawara

Babban Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara game da harkokin satar dukiyar Gwamnati watau Farfesa Itse Sagay ya fadawa Jam’iyyar APC za ta iya shan kasa zabe mai zuwa idan tayi sake.

Muddin APC ta ki sauraran Gwamnonin ta, to za a sha kashi a hannun PDP – Mai ba Buhari shawara

Sagay yace idan APC tayi wata-wata za a koma gidan jiya
Source: Facebook

Labari ya zo mana daga Jaridar Concise News cewa Itse Sagay ya fadawa Jam’iyyar APC mai mulki ta guji amfani da tsarin zaben kato-bayan-kato a 2019. Mai ba Shugaban kasar shawara ya nemi APC ta yi wa Gwamnonin ta biyayya.

Gwamnonin Jihohi da-dama ba za su so ayi irin wannan ‘yar tinke a zaben 2019 ba, don haka ne Sagay ya nemi Jam’iyyar ta bi ta Gwamnonin na ta idan har ta na son samun nasara a zabe mai zuwa ko ta sha kashi a hannun Jam'iyyar PDP.

KU KARANTA: PDP ta soki Kungiyar da ta sayawa Buhari fam din takara

Sagay wanda yana cikin masu ba Shugaba Buhari shawara ya nuna cewa idan har Gwamnoni APC su kayi wa Gwamnatin Tarayya bore za a iya samun babbar matsala a 2019. Dalilin wannan ne Sagay ya nemi a saurari Gwamnonin.

Gwamnoni sun nemi ayi amfani da tsarin ‘delegates’ ko kuma a samu hadin-baki wajen tsaida ‘Yan takaran 2019. Farfesa Itse Sagay yayi kira ga APC tayi duk rawan da Gwamnonin ke so ko kuma PDP ta tika ta da kasa a zaben badi.

Yanzu dai Uwar Jam’iyya ta ba Jihohi karfin gudanar da duk irin tsarin zaben da su ka ga dama wajen tsaida ‘Yan takara. Wannan ya sa irin su Sanata Shehu Sani su ka caccaki Jam’iyyar APC din.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel