An raba kan ‘Yan Najeriya a Gwamnatin Buhari – Saraki

An raba kan ‘Yan Najeriya a Gwamnatin Buhari – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya nuna cewa an raba kan ‘Yan Najriya a halin yanzu da sunan addini da banbancin kabila. Tsohon Gwamna Saraki dai ya fito takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP.

An raba kan ‘Yan Najeriya a Gwamnatin Buhari – Saraki

Bukola Saraki yace Buhari yayi karshen abin da zai iya a mulki
Source: Facebook

Bukola Saraki ya leka Kudancin Najeriya inda yake cigaba da kamfen na samun lashe zaben fitar da gwani da Jam’iyyar PDP za tayi kwanan nan. Saraki ya bayyana cewa abubuwa sun tabarbare yanzu ta ko ina a Najeriya.

Shugaban Majalisar Kasar yayi wannan jawabi ne lokacin da ya ziyarci manyan PDP a Jihar Enugu inda ya bayyana cewa ba ra’ayin kan sa ta say a fito neman kujerar Shugaban kasa a 2019 ba illa don ya ceci Najeriya a 2019.

KU KARANTA: Yadda Gwamnatin Buhari ke kokarin samawa Talakawa gidaje a Najeriya

Saraki yana ganin cewa Shugaba Buhari yayi duk iyaka kokarin da zai iya a Gwamnati sai dai kokarin Gwamnatin ta sa bai kai ko ina ba. Saraki ya bayyanawa ‘Ya ‘yan PDP cewa ‘Yan Najeriya sun shiga wani mawuyacin hali.

Babban ‘Dan Majalisar ya koka da yadda matasa ke fama da rashin aiki a Najeriya don haka ne yace yake neman zama Shugaban kasa. Shugaban Majalisar yayi alkawarin shawo kan matsalolin kasar nan idan aka zabe sa a 2019.

Dama ka na da labari cewa PDP ta samu hada-kan manyan ‘Yan siyasar da su kayi takarar fitar da gwani na Gwamnan Jihar Osun. Yanzu dai Ademola Adeleke da Akin Ogunbiyi sun amince su yi aiki tare bayan Saraki ya sa baki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel