APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

- A jiya, Alhamis, ne jam’iyyar APC ta gudanar da taron gangamin yakin neman zaben dan takarar ta a jihar Osun

- Saukar jirgin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta saka farinciki a wurin jama’ar da suka halarci taron a garin Osogbo

- Za a yi zaben gwamna a jihar Osun ranar 22 ga watan Satumba, da muke ciki

A jiya, Alhamis, ne jam’iyyar APC tayi taron gangamin yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna a jihar Osun.

Jirgin dake dauke da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sauka a filin taron gagamin kamfen din jam’iyyar APC a birnin Osogbo na jihar Osun.

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

Taron APC a jihar Osun
Source: Twitter

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

Jama'a a wurin taron APC a jihar Osun
Source: Twitter

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

Taron APC a jihar Osun
Source: Facebook

Ana sanar da saukar jirgin Osinbajo da misalign karfe 4:05 na rana sai jama’ar dake wurin taron suka kaure da sowa da farinciki tare da nufar inda jirgin ya sauka.

DUBA WANNAN: Osinbajo ya karrama hazikan matan Najeriya da suka yi bajinta a kasar Amurka

Manyan ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka halarci taron sun yi tururuwa domin gaisawa da mataimakin shugaban kasar. Daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar da suka kewaye Osinbajo domin gaisawa da shi bayan ya sauka, akwai gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, shugabn masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran su.

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da shugabanta na kasa, Adams oshiomhole, gwamnoni da sanatoci da mambobin majalisar wakilai sun halarci taron.

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

APC tayi taro a jihar Osun
Source: Twitter

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

APC tayi taro a jihar Osun
Source: Facebook

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel