2019: APC Yobe ta ba Gwamna Gaidam ikon zabar wadda zai gaje shi

2019: APC Yobe ta ba Gwamna Gaidam ikon zabar wadda zai gaje shi

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) babin jihar Yobe ta ba gwamnan jihar mai shirin barin mulki, Mista Ibrahim Gaidam zabi na dan takaran da zai gaje shi a zaben 2019.

Mambobin jam’iyyar a wata ganawa da suka yi a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba sun amince da cewar za’a fitar da dan takaran jam’iyyar a zaben 2019 ta zaben wakilai ko na kato-bayan-kato.

Maganar karshe da aka tsaya akanta dauke da sa hannun mataimakin gwamna, Abubakar Aliyu shine cewa za’a ba Gwamna Gaidam damar yanke shawara akan wadda zai tsaya takaran kujerar gwamnan APC a jihar.

2019: APC Yobe ta ba Gwamna Gaidam ikon zabar wadda zai gaje shi

2019: APC Yobe ta ba Gwamna Gaidam ikon zabar wadda zai gaje shi
Source: Depositphotos

Shugabannin APC sun kuma ba gwamnan tikitin takaran kujeran sanatan Yobe maso gabas a zabe mai zuwa ba tare da dan adawa ba.

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ya lalata gidaje sama da 5,000 a Sokoto, Kebbi da Zamfara - NEMA

Tsohon gwamnan jihar, Bukar Abba Ibrahim wadda bai halarci ganawar ba shine ke rike da kujerar sanata na yankin Yobe maso gabas a yanzu.

Mista Ibrahim ke rike da kujerar tun bayar da ya sauka daga gwamna a 2007.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel