Da dumi-dumi: Allah ya yiwa mahaifin bulaliyar majalisa, Ado Doguwa, rasuwa

Da dumi-dumi: Allah ya yiwa mahaifin bulaliyar majalisa, Ado Doguwa, rasuwa

Allah ya yiwa mahaifin bulaliyar majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, Alhaji Garba Doguwa rasuwa a yau Alhamis, 6 ga watan Satumba, 2018.

Shugaban tawagar kiwon lafiyan aikin hajjin 2018, Ibrahim Kana, ya tabbatar da cewa Alhaji Garba Doguwa ya rasu ne da yammacin yau a asibitin King Abdulazeez da ke birnin Makkah, kasar Saudiyya.

Yace: “Ina tabbatar da cewa ya rasu ne yau a asibitin King Abdulazeez da ke Makkah. Ya kasance cikin rashin lafiya,”.

Alhaji Garba Doguwa ya kasance cikin tawabar mahajjatan gwamnati a hajjin bana.

Allah ya jikansa da rahama.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel