Kwamitin amintattu na PDP ta gargadi mambobinta akan dinkewa da yan takaran kujerar shugaban kasa

Kwamitin amintattu na PDP ta gargadi mambobinta akan dinkewa da yan takaran kujerar shugaban kasa

- Kwamitin amintattu na jam’iyyar tayi kira ga mambobinta da babban murya

- Ta gargade su akan dinkewa da yan takaran kujerar shugaban kasa

- A cewar Sanata Walid Jibrin hakan na iya haifar da rikici

Kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gargadi mambobinta akan dinkewa da yan takaran kujerar shugaban gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar da za’a gudanar a ranar 6 ga watan Oktoba.

Da yake jawabi ga manema labarai a taron gaggawa da suka gudanar a Transcorp Hilton dake Abuja a ranar Alhamis, shugaban kwamitin, Sanata Walid Jibrin ya ce gargadin ya zama dole domin gujema barkewar rikici.

Kwamitin amintattu na PDP ta gargadi mambobinta akan dinkewa da yan takaran kujerar shugaban kasa

Kwamitin amintattu na PDP ta gargadi mambobinta akan dinkewa da yan takaran kujerar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Jibrin yace wasu daga cikin mambobin kwamitin a lokacin takaran jam’iyyar na 2017, sun nuna fifiko akan yan takara wadda ya sabama zaton jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Idan makamai kuke nema ku tafi Sambisa – Shehu Sani ga yan sanda

Ya sanar da cewar taron ta tsawaita wa’adinsa wadda ya lalace da shekaru biyar yayin wani tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara wadda ya zamo sakataren kwamitin bayan dakatar Ojo Madueke ma ya samu tabbacin Karin shekaru biyar domin gudanar da aiki a wannan kujerar.

Ya kuma sanar da cewa kwamitin amintattun ta kuma kafa wata kwamiti domin tattaunawa day an takara daban-daban domin samun fahimta akan harkokin yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel