2019: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC

2019: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC

- Jam'iyya mai mulki ta APC ta sake caccakar shugaban majalisar dattijai, inda ta bayyana kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa a matsayin 'Almara'

- Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Mr. Yekini Nabena, ya ce shekaru 8 da Saraki yayi a matsayin gwamnan jihar Kwara, aya ce ga yan Nigeria

- Da ya ke maida martani, Saraki ya ce ba zai tsaya yana fada da Kakakin jamiyyar APC ba, sai dai idan iyayen gidansa sun isa, to su fito a kara

Jam'iyyar APC ta sake caccakar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, tana mai cewa kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa kamar wata almara ce, ko kuma kanzon kurege.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Yekini Nabena, ya yi wannan gugar zanar a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, a ranar laraba.

Jam'iyyar ta ce duk da cewar yanci ne ga duk dan Nigeria ya tsaya takarar shugaban kasar, tana cike da zullumi na cancanta, nagarta da kuma kaifin basirar jagorantar lamuran kasar.

APC ta ce bata da wata masaniya akan tuggun da ke cikin tsayawa takarar shugaban kasa da Saraki ya bayyana, musamman don karkatar da hankulan al'umma daga irin abubuwan da suke faruwa a majalisun tarayya na kasar.

2019: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC

2019: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa

Sanarwar ta yi nuni da cewa, shugabancin da Saraki yayi a shekaru 8 da ya kwashe yana gwamnan jihar Kwara, abun ya zama darasi ne ga al'umar kasar.

Sai dai da ya ke maida martani, Saraki nemi ba'asi akan dalilin da ya sa APC da sakaren watsa labaranta na kasa suke masa shigar sharo ba shanu tun bayan da ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyar PDP.

Saraki, a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar laraba, ta hannun mai bashi shawara na musamman kan kafafen watsa labarai, Mr. Yusuph Olaniyonu, ya bayyana cewa ba shi da wata matsala da ta shafi kwarewar shugabanci kamar yadda APC ta yi ikirari.

Sanarwar tace: "Shugaban majalisar dattijai ba zai maida hankali ga wasu tsiraru da ke son kawo rudani a cikin siyasar sa ba, haka zalika ba zai biyewa wani da ke zaune a Abuja yana jira a rubuta sanarwa daga Legas a tura mashi don ya buga da sunansa ba. Idan har iyayen gidansa sun isa, to su fito a kara da su"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel