PDP ta ga baiken sayawa fam din takara

PDP ta ga baiken sayawa fam din takara

- Jam'iyyar PDP ta soki kungiyar da ta siyawa Buhari fam inda ta ce yaudara ce kawai ake yiwa talakawa

- PDP ta kuma ce bawa dan takarar gudunmawa fiye da N1m ya sabawa dokar zabe saboda haka sayawa Buhari fam na N45m laifi ne

- PDP ta yi kira ga hukumar INEC ta gagauta hukunta shugaba Buhari muddin bai fito filli ya ki amincewa da saya masa fam din ba

Jam'iyyar adawa ta PDP tayi ikirarin cewa anyi amfani da wata kungiyar bogi ne domin siyawa shugaba Muhammadu Buhari fom din takarar zaben shugabancin kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan N45 miliyan.

Bayan siffanta wannan abin a matsayin 'yaudara da mutane sun gaji da ita', PDP ta ce lamarin na iya rage wa shugaba Muhammadu Buhari farin jini a wajen jama'a.

PDP ta ga baiken sayawa fam din takara

PDP ta ga baiken sayawa fam din takara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Miji na zargin matar sa da cin amana saboda ya ga kororon roba a jakar ta

A sanarwa da ta fito daga Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce shugaba Buhari ba zai iya yaudarar mutane da sunan cewa yana tare da talakawa ba.

"Mutane sun farga sun gano cewa shugaban kasa da na kusa dashi suna rayuwa cikin daula, alhalin ya yi watsi da miliyoyin talakawa da suka amince dashi suka bashi amana a 2015.

Kazalika, PDP ta janyo hankalin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) cewa sayawa shugaba Muhammadu Buhari fam da kungiyar tayi ya ci karo da sashi na 91(9) na dokar zabe da ya ce "ba'a amince mutum ko kungiya ta bawa dan takara tallafin da ya haura N1 miliyan ba."

"Tunda shugaba Buhari bai fito fili ya nuna kin amincewarsa da sayan fam din da kungiyar tayi masa, ya kamata INEC ta gurfanar da shugaban kasa cikin sa'o'i 24 kamar yadda dokar zabe ya tanada," inji PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel