Rayuka 2 sun salwanta a wani sabon hari da ya auku a jihar Filato

Rayuka 2 sun salwanta a wani sabon hari da ya auku a jihar Filato

Kimanin rayukan mutane biyu ne suka salwanta yayin aukuwar wani hari na 'yan bindiga da safiyar yau ta Alhamis cikin kauyen Nding Suisit dake karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP Terna Tyopev, shine ya bayar da tabbacin wannan lamari ga kamfanin dillancin labarai na Najeria cikin birnin Jos, inda ya ce mutane biyu sun jikkata yayin aukuwar harin.

Rayuka 2 sun salwanta a wani sabon hari da ya auku a jihar Filato

Rayuka 2 sun salwanta a wani sabon hari da ya auku a jihar Filato
Source: Twitter

Yake cewa, bayan aukuwar harin an garzaya da mutane hudun da tsautsayin ya ritsa da su babban asibitin garin Jos inda nan take likitoci suka tabbatar da mutuwar biyu daga cikin su yayin da a halin yanzu sauran biyun ke karbar maganida kulawa.

KARANTA KUMA: Mutane 6 sun shiga hannu bisa laifin lallasa wani Jami'in dan sanda a jihar Osun

Tyopev ya kara da cewa, hukumar na kuma ci gaba da gudanar da bincike kan wannan mummunan lamari yayin da tuni aka binne gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaiito cewa, a daren yau na Juma'a ne ake sa ran dawowar shugaban kasa Muhammmadu Buhari gida Najeriya tare da tawagar sa da suka kai ziyara kasar China domin halatar taron hadin kan kasar da kuma kasashen Afirka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel