Sauya jam’iyya ba tsere wa EFCC ba ne – Magu ga barayin yan siyasa

Sauya jam’iyya ba tsere wa EFCC ba ne – Magu ga barayin yan siyasa

- Shugaban EFCC, Ibrahim Magu yayi raddi ga barayin yan siyasa

- Yace sauye-sauyen sheka daga jam'iyyun siyasa ba zai kubutar dasu daga tuhumar hukumar ba

- Magu yace duk dan siyasan da suka kama da satar kudin gwamnati zai fuskanci shari'a

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu, ya bayyana cewa ‘yan siyasa da ke ta saue-sayen sheka daga jam’iyyun siyasa, ba za su iya guje ma hukumar daga gurfanar da duk wani cikin su wanda ya saci dukiyar gwamnati ba.

Da ya ke bayani a gurin taron tattaunawa yan jaridun kasar nan a Lagas, Magu ya ce babu wurin buya ga irin wadannan ‘yan siyasa, ballantana su samu mafaka daga kamu da bincike da kuma gurfanarwar da za’a yi musu.

Sauya jam’iyya ba tsere wa EFCC ba ne – Magu ga barayin yan siyasa

Sauya jam’iyya ba tsere wa EFCC ba ne – Magu ga barayin yan siyasa
Source: Depositphotos

Da ya ke mayar da martani ga wata tambaya da aka yi masa cewa jam’iyyar APC mai mulki na yin katsalandan a cikin aikin hukumar, Magu yace, bai taba samun wani umarni ko rokon yin wata alfarma ga wani bincike da hukumar sa ke yi ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku da magoya bayansa sun mamaye hedkwatar PDP

Magu cewa ya yi abin ya zama tamkar al’ada ga ‘yan siyasa idan ana binciken su sai su rika cewa ana yi musu bi-ta-da-kulli na siyasa.

Ya ce kafafen yada labarai na da hakkin a kan su kada su bari batagarin ‘yan siyasa su yi amfani da dukiyar da suka sata ta hanyar jan ragamar gwamnati irin yadda suka ga dama.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa dan majalisa mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani akan mamayar da wasu jami’an yan sanda suka kai gidan babban jigon kasar Edwin Clark dake Abuja.

Sani wadda ya soki yan sanda a shafinsa na Twitter akan harin da ya haifar da cece-kuce a fadin kasar yace yan sanda su tafi wani wuri neman makamai maimakon kai mamaya gidan da suka san abunda zasu samu mai wuce litattafai da sauran kayayyakin aikin gida ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel